Neman haihuwa ya sa Boka ya binne mace da ’yarta da ransu

Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta gabatar da wani boka, dan shekara 64 mai suna Alhaji Olatunji Azeez, wanda ya yi ikirarin kashe wata jami’ar hukumar kwastam mai ritaya, mai suna Misis Angela Kerry da ’yarta mai shekaru 10, mai suna Obiagulum, a ranar 10 ga watan Mayun shekarar da muke ciki.Aminiya ta gano cewa […]

Neman haihuwa ya sa Boka ya binne mace da ’yarta da ransu
Neman haihuwa ya sa Boka ya binne mace da ’yarta da ransu

Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta gabatar da wani boka, dan shekara 64 mai suna Alhaji Olatunji Azeez, wanda ya yi ikirarin kashe wata jami’ar hukumar kwastam mai ritaya, mai suna Misis Angela Kerry da ’yarta mai shekaru 10, mai suna Obiagulum, a ranar 10 ga watan Mayun shekarar da muke ciki.
Aminiya ta gano cewa sashen yaki da masu aikata manyan laifuka na rundunar ’yan sandan jihar Legas ya gano gawarwakin matar da ’yarta a gidan Azeez da ke layin Ire Akari a unguwar Ajuwon Akute da ke jihar Ogun.
Azeez, wanda dan asalin jihar Oyo ne, yana da matan aure uku da ’ya’ya biyar, ya ce tilas ce ta sa ya kashe Angela da ’yarta bayan da matar ta yi masa barazanar kasha shi a kan kudin da take binsa bashi.
Ya ce, ‘Ni mai maganin gargajiya ne. Na yi shekara 30 ina sayar da magani. Na hadu da Angela shekaru biyar da suka wuce. Ta zo wurina ne neman maganin kariya daga sammu. Wata kawarta mai suna Lizzy ita ta kawo ta wurina. Mun kulla alaka kuma ta rika zuwa wurina neman taimako daban-daban. Shekaru uku da suka wuce ta fada min tana da matsalar haihuwa, yarinyar da na gan su tare ba ’yar cikinta ba ce, na yi mamaki, amma da ta shaida mini shekarunta sai na gaya mata cewa ba za ta iya samun ciki ba saboda shekarunta sun wuce haihuwa, amma sai ta dage cewa limaman coci da yawa sun sanar da ita cewa za ta iya samu ciki.’
Ya ci gaba da cewa, ‘Da na ga ta ki yarda da abin da na gaya mata, sai na karbi Naira miliyan 10 daga hannunta saboda na san cewa idan ma ban karbi kudin ba za ta je inda za a karba kuma ba za ta samu biyan bukata ba. Na hada mata magungunan daukar ciki, amma ba su yi aiki ba saboda shekarunta. Bayan wata guda sai ta dawo tana korafin cewa sai na dawo mata da kudinta, ni kuma sai na gaya mata cewa ba zan biya ta kudin ba, sai ta fara yi mini barazanar za ta sa a kashe ni, sai na yi kokari na biya ta Naira miliyan biyu da rabi. A cikin makon da na biya ta, sai ta dawo tana neman na ba ta sauran Naira miliyan bakwai da rabi.’
Ya kara da cewa, ‘Ranar 17 ga watan mayu sai ta zo da ’yarta ta dage cewa sai na ba ta saura kudinta, ta rika cewa a matsayinta na jami’ar kwanstam za ta ita kashe ni idan ban biya ta sauran kudinta ba. Ni kuma sai ga cewa ya kamata na kashe ta kafin ta kashe ni. Sai na haka rami mai zurfi a bayan gidana, sai na rufe da tabarma da farin kyelle, kamar dakina na bokanci, tana zuwa gidan sai na ja ta wurin da niyyar mu je mu yi addu’a, muna zuwa kusa da ramin sai na ce mata ta tsuguna tare da ’yarta mu fara addu’a, suna hawa kan ramin sai kawai suka zurma ciki da ’yar tata. Da na leka sai ganta a zaune ita kuma ’yar a tsaye. Nan da nan sai na rika zuba kasar da na fitar daga cikin ramin, na rika zubawa a kansu har sai da na binne su da ransu. Na zuba kamar bokiti 50 ko fiye na kasa a kansu, bayan na kwashe jakunkunansu da sauran kayan da suka zo da su na boye. Washe gari na nemo birkiloli suka simince wurin, ba tare da sun san abin da ke ciki ba.’
Kwamishinan rundunar ’yan sandan jihar Legas, Umar Manko ya bayyana cewa ’yan sanda sun kammala bincike a kan lamarin, sai dai za su mika wanda ake zargi a kotu kan zargin kisan kai.
Ya ce, “tun ranar 10 ga watan Mayun shekarar da muke ciki dangin matar suka  sanar da ’yan sanda cewa suna cigiyarta. Daga bisani mun kama wanda ake zargi ta hanyar na’urar da ke motar marigayiyar kirar Toyota Kamri. Azeez ya dade yana zaluntar matar. Ya karbi kimanin Naira miliyan 20 daga wurinta da suka hada da kudi da kadarori. Mun gano cewa ya haka rami ne a wani daki da ke cikin gidansa inda ya ja matar da ’yarta ciki da dabara, bayan sun fada cikin ramin ya binne su da ransu. Mun gano gawarwakin, mun dauko kayansu da ya binne su tare. Mun  kammala bincikenmu za mu gurfanar da shi a gaban kotu kan kisan kai. Za mu bar komai a hannun kotu don ta yi hukunci.’