Neman hana ’yan shekara 17 sayen layin waya ya yamutsa hazo
NCC ta ce an yi wa batun kayyade shekarun sayen layin waya mummunar fahimta.
Ra’ayoyin ’yan Najeriya sun bambanta game da yunkurin Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) na haramta wa masu kasa da shekara 18 sayen layin waya.
’Yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu mabanbanta game da matakin na NCC, wanda zai haramta wa kamfanonin sadarwa yi wa masu kasa da shekara 18 rajistar mallakar layin waya nan gaba.
- Kudin e-Naira: Ma’ana, fa’idoji da tsarin gudanuwarsa (1)
- Najeriya A Yau: ’Yan Siyasa Na ‘Buya’ Saboda IPOB A Anambra
A halin yanzu dai NCC na kan aiki ne a kan daftarin sabuwar dokar wadda tuni ta aike wa kamfanonin sadarwa bukatar su turo mata ra’ayinsu da shawarwari a kai.
Kwafin daftarin dokar da aka NCC ta wallafa a shafinta ya nuna, “Dole sai mutum ya kai shekara 18 kafin ya iya mallakar layin waya daga daya daga cikin kamfanonin sadarwa.”
-
– Ra’ayoyin ’yan Najeriya
’Yan Najeriya da dama na ganin matakin da hukumar ta dauka ya yi daiadai saboda zai taimaka wajan rage amfani da wayoyi barkatai, tare da rage rage yaduwar matsalolin tsaro a kasar.
Ibrahim Iro Wudil na ganin cewa wannan tsari ne da ya tun tuni ya kamata a yi , kamar yadda ya wallafa a Facebook.
Shima Abdulhafiz Yakubu Muhammad yace “yin hakan daidai ne ganin yadda matasa maza da mata suke yin abin da bai kamata ba.”
Wasu ’yan Najeriya kuma, musamman ’yan kasa da shekara 18 na ganin matakin bai dace ba. A cewarsu, hakan zai katange su daga amfani da wayoyin hannu wanda ba karamin nakasu zai kawo ga rayuwarsu ba.
-
– Martanin kamfanonin sadarwa
Babban kamfanin sadarwa na MTN ya nuna rashin gamsuwa da wannan mataki da NCC ke shirin dauka.
A nasa bangaren shekara 18 sun yi yawa, don haka kamfanin ya bukaci a mayar da shekaru mafi karanci ya iya mallakar layin waya zuwa shekara 14.
-
– Abin da masana suka ce
Masana dai na ganin matakin na NCC na iya kawo koma baya a ci gaban fasahar sadarwar zamani (ICT) da kuma tattalin arzikin kasar.
Amma wasu daga cikinsu suna ganin sharadin cika shekara 18 din ya dace da sauran tsare-tsaren mallakar lasisi a Najeriya.
Wasu kuma na ganin abin da ya fi dacewa shi ne a mayar da dokar ta koma daga shekara 15 zuwa abin da yayi sama.
-
– NCC ta kara bayani
A wani bayani da ta fitar ta hannun Daraktan Yada Labaranta, Ikechukwu Adinde, NCC ta masunanta cewa tana neman haramta wa masu kasa da shekara 18 mallakar layin waya.
Ta bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya kayyade shekara 18 a matsayin shekarar ‘taklifi’.
Ta ce doka ce ta tsara cewa kafin ulla yarjejeiniya ko cinikin mallakar layin waya tsakanin kamfanin sadarwa da mai sayen layin, wajibi ne bangarorin su mallkai hankalin kansu ta yadda za su dauki alhakin sun abin da ya faru a sakamkon yarjejeniyar da ke tsakaninsu.
Don haka, hukumar ta ce dokar na kokari ne na tabbatar da kariya ga kananan yara, ta yadda iyayensu ko waliyyansu za su iya sayen layin waya da sunayensu su ba wa yaran, kuma su za a kama da alhakin duk abin ya ya biyo baya a sakamakon amfani da yaran suka yi da layukan.
Saboda haka ta ce, matakin wanda ake shirin dauka bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki zai taimaka wajen karfafa bangaren tsaron kasa.