‘Neman suna ya sa aka kirkiro Miyetti Allah Kautal Hore’
Alhaji Baba Othman Ngelzarma shi ne Sakataren kungiyar Fulani Makiyaya wadda ake kira Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na kasa. A hirar da Aminiya ta yi da shi a Abuja a makon jiya, ya bayyana yadda kungiyarsu take gudanar da ayyukanta da kuma kalubalen da take fuskanta. Ga yadda tattaunawar ta kasance: […]
Alhaji Baba Othman Ngelzarma shi ne Sakataren kungiyar Fulani Makiyaya wadda ake kira Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na kasa. A hirar da Aminiya ta yi da shi a Abuja a makon jiya, ya bayyana yadda kungiyarsu take gudanar da ayyukanta da kuma kalubalen da take fuskanta. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Za mu fara da gabatar da kanka..
Baba Othman: Assalamu alaikum, sunana Baba Othman Ngelzarma. Ni ne Sakataren kungiyar Fulani Makiyaya wadda ake kira Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na kasa.
Aminiya: A kwanakin baya an yada jita-jitar cewa kungiyarku ce ta shiga ta fita har aka dakatar da shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore Alhaji Bello Badejo saboda shi kadai ne ya tsaya wajen ganin ya kwato wa Fulani hakkokinsu, ganin hakan ne ya sa kuka dauki wannan matakin. Me za ka ce a kan hakan?
Baba Othman: Ita magana idan mai yinta wawa ne mai sauraren ta ba zai zama mahaukaci ba. Kamar yadda nake so ka sani an yi wa kungiyarmu (MACBAN) rijista fiye da shekara 30. Iyayen kungiyarmu sun hada da Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubukar, wanda shi ne shugaban iyayen kungiyarmu. Mambobin sun hada da Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na II, shi ne ya gaji wannan kujera daga wurin marigayi Ado Bayero, akwai Sarkin Zazzau Alhaji Kabir Usman da Lamidon Adamawa Alhaji Muhammad Barkindo Mustapha da kuma Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman. Idan ka duba wadanda suke jagorantar kungiyar, to babu dalilin da za a ce wata jaririyar kungiyar da ba ta wuce shekara uku zuwa hudu ba a ce za ta tsole mana idanu. Ina so mutane su gane Kautal Hore an kirkiro ta ne don biyan bukatar kai. shi kansa shugabanta ba zabar sa aka yi ba. kungiyar ba ta da kyakkyawar manufar da za a ce har mun damu da ita ba. Yana so ya yi suna ne, kuma ka san an ce idan kana so ka yi suna sai ka zagi gwani. Ba mu san yadda aka dakatar da shi ba, ba mu san yadda suke gudanar da ayyukan kungiyarsu ba.
Aminiya: An ce tun da dadewa aka yi wa kungiyarku rijista amma kun kasa magance rikicin Fulani da manoma, inda Kautal Hore cikin kankanen lokaci ta shawo kan wannan rikici, inda ta bayyana ta samu wannan nasarar ne sakamakon kusantar gwamnati da ta yi, shin me ya sa ba kwa kusantar gwamnati?
Baba Othman: Ina so mutane su sani a watan Maris, 2014 muka yi zabe a karkashin umarnin Sarkin Musulmi. Bayan mun kammala zabe ne ya kaddamar da mu a fadarsa. Nasararmu ta farko ita ce, yadda muka hada gwamnonin Arewa 19 a Abuja, muka tattauna abubuwan da suka shafi Fulani. Mun tattauna halin da Fulani suke ciki a kowace jiha. Gwamnonin sun fahimci abin da ake so su fahimta dangane da matsalolin Fulani. Mun yi taron kara wa juna sani na kusan Afirka gaba daya, inda ofishin Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya dauki nauyi. Kashi 90 cikin 100 na mutanen da aka gayyata daga MACBAN ne, an yi taron na kwana uku. Shugaban kungiyarmu ne ya yi magana da yawun kowace kungiyar Fulani. A nan gwamnatin Tarayya ta fahimci halin da Fulani suke ciki da kuma bukatunsu. Kusancinmu da gwamnati ne ya sa aka yi haka.
Bayan haka, Jihar Benuwai tana tsanantawa a kan abin da ya shafi Fulani, saboda rikicin da ya faru a jihar, wanda shi ya shafi Jihar Taraba da Filato da Nasarawa. Mun ziyarci Jihar Benuwai kusan sau shida mun zauna da gwamnan jihar, yanzu rikicin ya yi sauki, da zarar gwamnan ya ji wata matsala zai gayyace mu, kuma cikin ikon Allah idan mun je sai ta zama tarihi. A yanzu akwai kwamiti na Tibi da matasan Fulani don samar da zaman lafiya, su ne suke sintiri don hana barkewar rikici, idan kuma an samu matsala idan Tibi ne masu laifi a ba su, haka ma idan Fulani ne, a yi hukunci. bayan nan akwai kwamitin dattawa, da haka ne muka samo hanyoyin da muka magance rikicin Fulani da Tibi a Jihar Benuwai, inda aka samu lafiya a Filato da Taraba da kuma Nasarawa. Idan da sauran gwamnoni za su kamar yadda Gwamnan Jihar Benuwai yake yi da yanzu an shawo kan matsalar. Haka ma a Jihar Zamfara mun yi kokari wanda a yanzu su ma matsalar ta lafa, matsalar da ta rage a can ita ce ta satar shanu, ita ma muna ta kokarin ganin yadda za a shawo kan ta. Jihar Kaduna da Katsina ne gwamnoninsu ba su zauna da mu a jiharsu ba, amma duk da haka mun yi iya bakin kokarinmu wajen ganin mun takaita rikicin. Ina so a gane harkokin kungiya muka sa a gaba. Babu yadda za a yi mu gudanar da harkokinmu ba tare da gwamnati ko jami’an tsaro ba. Saboda zama da gwamnati ne ma ya sa aka kirkiro ma’aikatar Forestry and Libestock a Jihar Kebbi da Gombe da Neja da sauransu.
Aminiya: A yanzu wadanne matsaloli kuke fuskanta?
Baba Othman: Babban kalubalen da muke fuskanta shi ne wajen wayar da kan Fulani, yawanmu ya kai kusan miliyan 30 a Najeriya kawai, kuma yawancinmu muna zaune a cikin daji, wannan yawan ya kai yawan mutane na wadansu kasashen Afirka 3 zuwa 4, kalubalen shi ne yadda za su fahimci rayuwa a zamanance. kalubale na biyu shi ne, yadda Fulani za su samu ilimi, duk da cewa gwamnatocin da sun kirkiro Hukumar samar da ilimi ga Fulani, yanzu hukumar ta zama ta je-ki-na-yi-ki ne, ba ta samun kudin da take gudanar da harkokinta. Ina so gwamnati ta fahimci idan ta ba Fulani ilimi matsalolin da suke fama da su za su ragu, domin ilimi na wayar da kan dan Adam, yana sa imani. bafulani wayayye ne, zai taso daga kasar Mali, ya shiga Kamaru da Nijar da Burkina Faso zuwa Najeriya, ya hadu da mutane daban-daban.
Wani kalubalen shi ne, yadda za mu koyar da Fulani dabarun kiwo, domin shi muka gada, mutanmu nono suke sayarwa, da kuma yadda gwamnati za ta fahimci muhimmancin kiwo don ta inganta shi, wato gwamnati ta kawo tsarin da Fulani za su sayar da dabbobinsu ba tare da wahala ba. Mun fada wa gwamnati zai yi wahala a zaunar da Fulani a wuri daya tashi daya, saboda sun dauki yawon a matsayin al’ada. kafin ka raba su da al’adar sai ka nuna musu wannan abin ya fi al’adarsu muhimmanci. Idan ka kebe Bafulatani a daji, ka zuba masa irin ciyawa da dabbobinsa za su ci a shekara, sannan ka yi masa dam din da dabbobinsa za su sha ruwa, sannan ka gina masa makaranta a wurin, ka kuma rika ilimantar da shi dabarun kiwo na zamani, na tabbata babu inda zai je. Wani kalubalen kuma shi ne rashin kudi, domin ba mu gaji ko kobo a asusun kungiya ba, amma haka muke ta tutturawa.
Aminiya: Wane yunkuri kuka yi wajen magance satar shanu?
Baba Othman: A yanzu mun kirkiro wata hanya ta samar da kudin shiga da kuma magance satar shanu, wannan hanya ita ce kowace saniya akwai kudin da aka biya mata sannan a ba ta rasit a kungiyance, inda ko an kai ta Legas sai an bukaci wannan rasit din kafi a sayar da ita, ka ga hakan ya takaita satar shanu.
Aminiya: Daga karshe wane kira kake da shi ga Fulani?
Baba Othman: Ina so su fahimci duk inda Bafulatani yake ba zaman banza yake yi ba, yana tafiya da dukiyarsa ne a daji, idan rikici ya barke shi ne zai yi asara, za a kashe shi, ko a kashe dabbobinsa, don haka Fulani su lura da hakan, su kuma guji rikici. Su kasance masu bin doka da oda, sannan su yi kokarin sa ‘ya’yansu a makaranta.