Nenadi da Fani-Kayode sun yi zaman kurkuku na kwana uku
A ranar Talatar da ta gabata ce Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi a Legas Mai shari’a Sule Hassan ya tura tsohuwar Ministar Kudi, Misis Nenadi Usman da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode gidan yari bisa bayan da aka gurfanar da su a gabansa kan zargin almundahana da satar kudin gwamnati.Hukumar Yaki […]
A ranar Talatar da ta gabata ce Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi a Legas Mai shari’a Sule Hassan ya tura tsohuwar Ministar Kudi, Misis Nenadi Usman da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode gidan yari bisa bayan da aka gurfanar da su a gabansa kan zargin almundahana da satar kudin gwamnati.
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ce ta gurfanar da tsofaffin ministocin biyu tare da wadansu da suka hada da danjuma Yusuf da wani kamfani mai suna, Jointrust Dimensions Nigeria Limited, tana tuhumasru da aikata laifuffuka 17 da suka hada da hada baki da yin sata da cin hanci da kuma sanyawa a biya kudin da ya haye umarnin doka.
Misis Nenadi Usman ita ce daraktar kudi na Kwamitin Yakin Zaben Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a zaben bara, yayin da Fani-Kayode ya kasance daraktan watsa labarai na kwamitin.
Ana zarginsu da sacewa tare da raba kimanin Naira biliyan 4 da miliyan 900 mallakar Gwamnatin Tarayya.
Tsofaffin ministocin biyu dai sun musanta zargin da ake yi musu, lamarin da ya sa Alkali Sule Hassan ya bayar da umarnin a tsare su a kurukuku zuwa yau domin duba batun belinsu kamar yadda lauyan Fani-Kayode, Mista Ayo Adedipe (SAN) da lauyan Nenadi S. I. Ameh (SAN) da lauyan danjuma Yusuf, Mista Fred Orbih suka nema.
Lauyan Hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo ya nemi kotun ne ta bari a fara shari’arsu, amma lauyoyin wadanda ake zargi suka a fara sauraren batun belinsu tukunna.
Bayan kotun ta yanke wannan shawara ne sai jami’an gidan yari maza da mata suka wuce da su wani karamin gidan yarin da ke kusa da kotun. Kuma a daidai lokacin da ake fita da su daga kotun an ga fuskar Fani-Kayode a turbune, yayin da Nenadi ta rika amfani da hankici tana share fuskarta.
Daga baya an kai Fani-Kayode da danjuma kurkukun Ikoyi a karkashin tsattsauran tsaro, yayin da aka wuce da Nenadi kurkukun kirikiri, saboda babu bangaren mata a kurkukun Ikoyi.