NERC ta hana kamfanin Disco mallakar hannun jari a kamfanonin raba mita
Ma’aikatar Lura da kamfanonin wutar lantarki ya dakatar da kamfanonin raba wutar lantarki da wadanda suka sanya hannun jari da kamfanonin da ke karkashinsu da daraktocinsu da kuma wadanda suke da alaka da su daga mallakar hannun jari a kamfanonin samar da mitar wuta. Wannan ummarnin na kunshe ne a dokokin kamfanonin samar da […]
Ma’aikatar Lura da kamfanonin wutar lantarki ya dakatar da kamfanonin raba wutar lantarki da wadanda suka sanya hannun jari da kamfanonin da ke karkashinsu da daraktocinsu da kuma wadanda suke da alaka da su daga mallakar hannun jari a kamfanonin samar da mitar wuta.
Wannan ummarnin na kunshe ne a dokokin kamfanonin samar da mitar wadanda ake kira MAP a takaice wadanda za su taimaka wa kamfanonin samar da mita cikin sauki.
Dokokin sun nuna cewa manyan jami’an kamfanonin raba wuta na Disco kada su rike matsayi na darakta ko manyan mukaman kafanonin samar da mitar.