Netanyahu ya kori babban hadiminsa kan kalaman nuna wariyar launin fata
Naɗin Norden ya zo ba zato ba tsammani, domin a baya-bayan nan Netanyahu ya nuna goyon bayan ci gaba da zaman Agmon a muƙamin.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya kori muƙaddashin babban hadiminsa bayan zargin furta kalaman wariyar launin fata da suka janyo ce-ce-ku-ce.
Netanyahu ya sanar cewa Ziv Agmon zai bar muƙaminsa nan da kwanaki masu zuwa, bayan naɗa Ido Norden a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
- Ana nuna damuwa kan sabon ƙudurin dandaƙe masu yi wa yara fyaɗe a Malawi
- An kashe ɗalibi a bikin sabbin ɗalibai a Jami’ar Neja
Rahotanni sun ce Agmon ya tayar da ƙura ne bayan an fallasa kalaman da ya yi, inda ake zarginsa da kiran Yahudawa ’yan asalin Morocco da sunan marasa mutunci, tare da sukar ‘yan jam’iyyar Likud da iyalan firaministan.
Naɗin Norden ya zo ba zato ba tsammani, domin a baya-bayan nan Netanyahu ya nuna goyon bayansa ga ci gaba da zaman Agmon a muƙamin.
Sai dai sabon wanda aka naɗa, Ido Norden, shi ma na fuskantar suka, bayan wasu ‘yan jarida sun ruwaito cewa ya ƙirƙiri shafin bogi a dandalin X domin tallata littafinsa da ke bayyana gazawar Isra’ila dangane da harin da Hamas ta ƙaddamar a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Har yanzu ana jiran tantance naɗin nasa daga hukumar tsaron cikin gida ta Isra’ila, Shin Bet.
Wannan sauyi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rikice-rikice da ce-ce-ku-ce a cikin ƙusoshin gwamnatin Netanyahu, ciki har da zarge-zargen da ke da alaƙa da yaƙin Gaza da kuma wasu batutuwan siyasa da ke janyo muhawara a ƙasar.