Netanyahu ya lashe zaben Isra’ila

A shekaranjiya Laraba ne Hukumar Zaben kasar Isra’ila ta bayyana Firaminista Benjamin Netanyahu matsayin wanda ya samu nasara a zaben gama-gari da aka yi a kasar ranar Talata. Bayan an kamala kirga yawancin kuri’un da aka kada, jam’iyyar Mista Netanyahu wato Likud, ta samu kujeru guda 30 a yayinda jam’iyyar adawa ta Zionist ke da […]

Netanyahu ya lashe zaben Isra’ila
Netanyahu ya lashe zaben Isra’ila

A shekaranjiya Laraba ne Hukumar Zaben kasar Isra’ila ta bayyana Firaminista Benjamin Netanyahu matsayin wanda ya samu nasara a zaben gama-gari da aka yi a kasar ranar Talata.

Bayan an kamala kirga yawancin kuri’un da aka kada, jam’iyyar Mista Netanyahu wato Likud, ta samu kujeru guda 30 a yayinda jam’iyyar adawa ta Zionist ke da kujeru 24. Wannan na nufin cewa firaministan zai iya kafa sabuwar gwamnatin hadin gwiwa ba tare da wata matsala ba.
Kuma zai yi mulki wa’adi na hudu kuma hakan ya nuna yadda ya samu farin jini daga baya, duk da cewar kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a na farko ta nuna cewa zai iya fadi zabe.
A kwanakin karshe na yakin neman zabe, ya yi wa masu tsattsauran ra’ayi alkawarin cewar ba zai “bari a samu kasar Falasdinawa mai cin gashin kanta ba.”
Wani babban jami’in Falasdinawa ya soki ‘yan Isra’ila da suka zabi mamaya Falasdinu a maimakon tattaunawar zaman lafiya.