Netanyahu ya yi kuskure game da makamashin nukiliyar Iran- Kerry
Sakataren tsaron Amurka John Kerry ya ce Firayi Ministan kasar Isra’ila ya yi kuskure dangane da matsayinsa game da shirin makamashin nukiliyar kasar Iran. John Kerry ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a taron kasashen duniya dangane da abin da ya shafi shirin makamashin nukiliyar kasar Iran a jiya Alhamis a Geneba.Idan […]
Sakataren tsaron Amurka John Kerry ya ce Firayi Ministan kasar Isra’ila ya yi kuskure dangane da matsayinsa game da shirin makamashin nukiliyar kasar Iran.
John Kerry ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a taron kasashen duniya dangane da abin da ya shafi shirin makamashin nukiliyar kasar Iran a jiya Alhamis a Geneba.
Idan ba a manta ba Netanyahu ya zargi Amurka da sauran kasashe duniya wajen gaza daukar matakin da za a hana Iran mallakar makaman nukiliya.
“Matsayin da Netanyahu ya dauka ba daidai ba ne, ya yi kuskure.” Inji Kerry.
Ana sa ran a makon gobe ne Netanyahu zai gabatar mukala a taron babbar jam’iyyar adawa ta Republican a Amurka.