Netherlands ta casa Senegal a Gasar Kofin Duniya

Sakamakon ya sa Netherlands ta zama ta daya a rukunin tare da Ecuador.

Netherlands ta casa Senegal a Gasar Kofin Duniya

‘Yan wasan Netherlands suna murna.

Kwallaye biyu da aka zura dab da za a tashi a wasa, sun bai wa Netherlands damar casa zakarun Afirka Senegal a ranar Litinin.

Wanna nasara dai ta bai ’yan wasan Louis van Gaal damar fara buga Gasar Kofin Duniya a Qatar da kafar dama.

An zura kwallayen ne a wasan a minti na 84 da farawa a rukunin A lokacin da dan wasan gaba, Cody Gakpo ya jefa kwallon farko a ragar Senegal, kafin daga baya Davy Klaassen ya ci ta biyu a karawar.

Ana dai ganin Senegal ba za ta yi wani katabus ba saboda ta rasa tauraron dan wasanta a wasan, sakamakon rauni wato Sadio Mane.

Kafin yanzu dai tawagar kasashen da ke rukunin A an yi hasashe cewa za su tashi kunnen doki babu ci, sai dai tuni lissafi ya sauya.

Ana saura minti shida, dan wasan gaban PSV Eindhoven Gakpo ya yi dirar mikiya a gaban golan Senegal Edouard Mendy.

Sakamakon ya sa Netherlands ta zama ta daya a rukunin tare da Ecuador, wacce ta doke Qatar mai masaukin baki da ci 2-0 a wasan farko na ranar Lahadi.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos