Neymar da Serena Williams da Kolo Toure sun shiga kamfe din UNICEF
Fitaccen dan kwallon kafar nan dan kasar Brazil, Neymar da fitacciyar ’yar kwallon Tennis ta duniya Serena Williams da fitaccen dan kwallon kafa na Afirka, Kolo Toure sun shiga kamfe din Hukumar Yara ta Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) mai taken “Babban Darasi na Duniya” don karfafa wa yara gwiwa su yi karatu.Wata sanarwa da ta […]
Fitaccen dan kwallon kafar nan dan kasar Brazil, Neymar da fitacciyar ’yar kwallon Tennis ta duniya Serena Williams da fitaccen dan kwallon kafa na Afirka, Kolo Toure sun shiga kamfe din Hukumar Yara ta Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) mai taken “Babban Darasi na Duniya” don karfafa wa yara gwiwa su yi karatu.
Wata sanarwa da ta fito daga Kakakin UNICEF a Najeriya, Geoffrey Njoku ce, ta bayyana haka, inda ta ce kasashe sama da 100 ne za su amfana da shirin koyarwar a karkashin shirin dorewar Bunkasa kasa na karni da Majalisar dinkin Duniya za ta amince da shi nan gaba a cikin watan nan.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka kaddamar da wannan kamfe a birnin New York, shirin da ake jin zai mayar da hankali kan yara da matasa a kokarin da ake yi na gina kyakkyawar makoma ga kowane dan kasa.
Tuni shirin ya samu goyon baya daga shugabanni da fitattun mutane a duniya da suka hada da Babbar Mashawarciyar UNICEF, Sarauniya Rania Al Abdullah ta Jordan da Jakadiyar UNICEF, Nancy Ajram da Serena Williams da Jakadan PLAN International Global, Freida Pinto da Dani Albes da Hrithik Roshan da Kolo Toure da Neymar da kuma Cibiyar Neymar Jr. Institute.
Shirin “Babban Darasi na Duniya -The World’s Largest Lesson- ba zai tsaya kan koyar da yara kan manufofin ci gaban duniya kawai ba ne, zai ma yi kokarin ganin ya tsoma su wajen ganin an cimma wadannan manufofi – da ilimantar da su kan kalubalen da suke barazana ga makomarsu tare da karfafa musu gwiwa su kawo canji a kashin kansu a cikin al’ummarsu,” inji Babban Daraktan UNICEF Anthony Lake.
Ya kara da cewa, “Matasa za su iya taimakawa wajen cimma wadannan manufofi ta hanyar sanya shugabanninsu su rika cika alkawuran da suka yi musu -da kuma tabbatar da suna gina kyakkyawar makoma ga kowa.”
Shirin zai rika gudana a ajujuwa a kowace nahiya a mako zuwa 28 a Satumba kuma ana jin yara maza da mata miliyan 500 da ke tsakanin shekara takwas da 14 za su samu damar sanin wani abu daga Manufofin Duniya da suka shafi kawo karshen mugun talauci a tsakanin mutane zuwa magance sauyin yanayi tare da ba dukkan yara damar samun ilimin firamare da sakandare. A karkashin shirin shugabannin gwamnati da ministoci a kasashe da dama za su koyar da darussa, da za su kunshi nunin majigi daga masana ilimi kan shirin yayin da Serena Williams da Kolo Toure da Neymar da Dani Albes suka yi tasu gabatarwar.