Neymar na kwadayin Real Madrid

Dan wasan Paris St Germain (PSG) na Faransa, Neymar ya ce zai iya komawa kulob din Real Madrid da taka-leda. Dan wasan ayarin Brazil, wanda aka saya da tsada fiye da kowa a tarihin kwallon kafa a duniya yana yin jinyar raunin da ya ji a yatsar kafarsa tun a ranar 23 ga  Janairun bana. […]

Neymar na kwadayin Real Madrid
Neymar na kwadayin Real Madrid

Dan wasan Paris St Germain (PSG) na Faransa, Neymar ya ce zai iya komawa kulob din Real Madrid da taka-leda.

Dan wasan ayarin Brazil, wanda aka saya da tsada fiye da kowa a tarihin kwallon kafa a duniya yana yin jinyar raunin da ya ji a yatsar kafarsa tun a ranar 23 ga  Janairun bana.

An dade ana alakanta Neymar, tsohon dan kwallon Barcelona da cewa zai koma Real Madrid bayan da PSG ta saye shi a shekarar 2013.

Neymar ya shaida wa gidan talabijin na Channel Globo ‘cewa ’Nan gaba, komai zai iya faruwa.’’ a wata tambaya da aka yi masa na yiwuwar komawarsa Madrid don ci gaba da kwallo.