Neymar na shirin komawa Saudiyya da murza leda
Tuni dan wasan ya fara tattaunawa da kungiyar da ke Saudiyya.
Dan wasan gaban Brazil da PSG, Neymar ya fara tattaunawa da kungiyar kwallon kafa ta Al-Hilal da ke Saudiyya don komawa can da murza leda.
Wata majiya daga PSG ta bayyana dan wasan mai shekara 31 a duniya ba ya daga cikin tsarin sabon kociyan kungiyar, Lius Enrique.
- Muna asarar N13bn duk mako saboda rufe iyakar Najeriya da Nijar – ’Yan kasuwa
- Sojojin Nijar Za Su Gurfanar Da Bazoum Kan Zargin Cin Amanar Ƙasa
Tuni dan wasan ya fara tattaunawa da kungiyar da ke Saudiyya don komawa can, inda zai dinga daukar albashi mai tsoka.
Har wa yau, majiya daga Al-Hilal, ta bayyana cewa da zarar ta kammala cimma matsaya kan dan wasan na Brazil za ta shiga tattaunawa da PSG kan farashin da za ta sayar da shi.
A watan da ya gabata ne Al-Hilal ta taya Kylian Mbappe Yuro miliyan 300, amma dan wasan ya ki amincewa da tayin da ta yi masa.
A watan Maris ne aka yi wa Neymar aiki a gwiwarsa, lamarin da ya sanya shafe watanni ba tare da yana yi wa PSG wasa ba.
Idan Neymar ya koma Saudiyya da murza leda zai bi sahun ‘yan wasan irin su Ronaldo, Benzema, Mane, Kante, Fofana, Alex Telles, Marcelo Brozovic da sauran.
A wannan kasuwar cinikayyar ‘yan wasannin ne ’yan wasa daga Turai suka dinga tururuwar komawa Saudiyya da murza kwallo.