Neymar ya yi ritaya daga buga wa Brazil tamaula
Neymar ya sanar da ritayarsa jim kaɗan bayan Brazil ta fice daga Gasar Kofin Duniya a daren ranar Lahadi.
Neymar Junior, ɗan wasa mafi shahara cikin taurarin ƙwallon ƙafa daga Brazil a zamanin nan, ya sanar da ritayarsa daga buga wa tawagar ƙasar tamaula.
Hakan dai na zuwa ne bayan tawagar Norway ta fatattaki Brazil daga Gasar Kofin Duniya ta 2026, wadda doke ta 2–1 a wasan zagayen ’yan 16 da suka fafata a ranar Litinin.
- Matashi ya kashe abokinsa da adda a Kuros Riba
- Harin Rasha ya yi sanadin mutuwar dalibar Najeriya a Ukraine
An ga ɗan wasan mai shekaru 34 ya zube a ƙasa yana kuka bayan tashi daga wasan wanda aka buga a birnin Meadowlands na Jihar New Jersey ta Amurka.
Kafin abokan tawagarsa su jajanta masa, kocin Brazil Carlo Ancelotti ne, ya miƙa masa hannu don ya jajanta masa.
Neymar ne ya zura ƙwallo guda da Brazil ta ci a wasan a bugun fenareti, amma hakan bai ceto Brazil ba, inda ita kuwa Norway ta wuce matakin kwata-fainal.
A nan na fara a nan na ƙare — Neymar
Da yake jawabi cikin jimami bayan tashi daga wasan, Neymar ya ce: “Na yi ƙoƙari. Na yi ƙoƙari. Na fara wasa a wannan filin wasa na MetLife Stadium, kuma a nan na ƙare. Yanzu dai komai ya ƙare.”
Ana iya tuna cewa Neymar ya buga wasansa na farko a tawagar Brazil a filin wasa na MetLife a ranar 9 ga watan Agustan 2010, a wasan sada zumunci tsakanin Brazil da Amurka.
Neymar ya yi ritaya ne a matsayin ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a Brazil, da ƙwallaye 80 a wasannin 130.
Ɗan wasan dai ya sha fama da rauni, wanda ya sa wasanni biyu kawai ya iya bugawa cikin biyar a gasar ta bana.
A matakin rukuni, minti 15 kacal ya buga a wasan da suka fafata da Scotland.
Neymar ya kasance mafi kyawun ɗan wasan Brazil sama da shekaru 10, duk da yawan jinya da ya yi ta fama da ita, wadda ta taƙaita tasirinsa.
Ya fara buga wa tawagar a 2010 bayan ya soma buga ƙwallon ƙwararru tare da Santos FC a 2009.
A 2016 Neymar ya lashe lambar zinare tare da tawagar a gasar Olympics.
Brazil dai ƙasa ce da ta shahara a fagen ƙwallo, kuma ita ce ta fi kowa lashe gasar inda ta ɗaga kofin har sau biyar a tarihi.