NFF ta ƙaryata dakatar da Osimhen

Har ya zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance da take nuna dakatar da ɗan wasan

NFF ta ƙaryata dakatar da Osimhen

ABIDJAN, IVORY COAST – FEBRUARY 2: VICTOR JAMES OSIMHEN of Nigeria during the TotalEnergies CAF Africa Cup of Nations quarterfinal match between Nigeria and Angola at Stade Felix Houphouet Boigny on February 2, 2024 in Abidjan, Ivory Coast. (Photo by Visionhaus/Getty Images)

Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta ƙaryata dakatar da ɗan wasan tawagar Super Eagles, Victor Osimhen.

Hukumar ta ce, labarin kanzon kurege ne kawai wasu daga cikin jaridu na intanet ke yaɗawa game da dakatar da ɗan wasan.

Jaridu da dama sun wallafa cewa NFF ta sha alwashin hukunta Victor Osimhen ne har sai ya bayar da haƙuri kan wani bidiyo da ya wallafa na caccakar tsohon kocin Najeriya Finidi George da ya ajiye aiki a bayan nan.

Babban Sakataren Hukumar, Dakta Mohammed Sanusi, ya bayyana mamakinsa da ganin yadda labarin ya yadu a wasu kafafen watsa labarai, inda ya ce har ya zuwa yanzu Hukumar ba ta kammala yanke hukunci kan dan wasan ba.

“Har ya zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance da take nuna dakatar da ɗan wasan.

“Abin da muka fi mayar da hankali a kai yanzu shi ne mu ga mun shawo kan matsalolin da suka dabaibaye tawagar ta Super Eagles,” in ji sanarwar.