NFF ta dage kungiyoyin kwallon da suka hada baki aka tashi 67-0 da 79-0 a shiyyar Bauchi

A karshen makon jiya ne aka samu labarin yadda wadansu kungiyoyin  kwallon kafa hudu suka hada baki da alkalan wasa aka tashi wasa da ci 67-0 da kuma 79-0 a shiyyar Bauchi a gasar rukuni-rukunin ’yan dagaji (Amateur).Su dai wasannin an yi su ne a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Bubayero FC da ke Gombe […]

NFF ta dage kungiyoyin kwallon da suka hada baki aka tashi 67-0 da 79-0 a shiyyar Bauchi

Alhaji Aminu MaigariA karshen makon jiya ne aka samu labarin yadda wadansu kungiyoyin  kwallon kafa hudu suka hada baki da alkalan wasa aka tashi wasa da ci 67-0 da kuma 79-0 a shiyyar Bauchi a gasar rukuni-rukunin ’yan dagaji (Amateur).
Su dai wasannin an yi su ne a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Bubayero FC da ke Gombe da kuma ta Plateau FC Feeder Team da ke Jos, a yayin da kuma aka yi wasa na biyu a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Akurba United FC da ke Nasarawa da kuma Police Machine da ke Adamawa.  Wasannin sun gudana ne a shiyyar Bauchi.
A wasannin zagayen farko da aka gudanar, kungiyar kwallon kafa ta Plateau Feeder Team ta doke ta Bubayero ne da ci 2-0 daga nan ta yi kunnen doki da ta Police Machine da ke Adamawa inda ta hada maki hudu.  Haka ita ma kungiyar kwallon kafa ta Police Machine ita ma ta hada maki hudu ne bayan ta lallasa ta Akurba United sannan ta yi kunnne doki da ta Plateau Feeder Team.
Don haka ake neman kungiyar da za ta haye zuwa gasar rukuni-rukuni aji na uku watau Dibision Three ne a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Plateau Feeder Team da kuma ta Police Machine.
A kan haka ne hukumar shirya wasan kwallon kafa ta kasa NFF ta sake shirya wasanni biyu a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa hudu watau “Play off” don tantance wacce za ta haye matakin gasa ta gaba (Dibision Three).
An gudanar da wasannin ne a ranar Alhamis ta makon jiya kuma a lokaci daya aka yi amma a filayen wasanni biyu da suka hada da na Games billage da  kuma na Abubakar Tafawa balewa dukkansu da ke Bauchi.
Sai dai abin mamaki shi ne yadda kungiyar kwallon kafa ta Police Machine ta lallasa ta Bubayero da ke Gombe da ci 67-0 yayin da kungiyar kwallon kafa ta Plateau Feeder Team ta lallasa ta Akurba United da ci 79-0. kungiyoyin sun yi haka ne don ganin daya daga ciki ta tserewa daya wajen hada maki da yawan kwallaye. Kuma duk wasannin biyu an tafi hutun rabin lokaci ne da sakamakon 6-0 da kuma 7-0.
To bayan an dawo hutun rabin lokaci ne guniyar kwallon kafa ta Police Machine ta zura kwallaye 61 yayin da ta Plateau Feeder Team kuma ta zuwa kwallaye 72 da hakan ya sa aka tashi ci 67-0 da kuma 79-0.
Jim kadan da tashi daga wasannin ne sai Kodinetan shirya gasar da ke shiyyar Bauchi, Honorabul Tanko Maiyaki ya yi fatali da sakamakon wasannin kuma ya bayar da sanarwar hukumarsa ta dage dukkan kungiyoyin kwallon kafar da alkalan wasan da kuma mataimakansu har sai baba-ta-gani.
Maiyaki ya ce hukumar NFF za ta kafa kwamitin bincike don tantance al’amarin kafin a dauki mataki.
A shekaranjiya Laraba ne Shugaban Kwamitin kula da yadda gsar ke gudana kuma Mataimakin shugaban hukumar na daya Mike Umeh ya bayar da umarnin a dage daukacin kungiyoyin kwallon da suka aikata wannan abin kunya tare da jami’ansu da kuma allakan wasan.
Daga nan ya umarci a daina yin wasa a shiyyar ta Bauchi har sai bayan an kammala bincike.
A tarihin wasan kwallon kafa a Najeriya, ba a taba samun sakamakon wasa irin wannan ba, don haka za a iya cewa kungiyoyin kwallon kafar sun kafa sabon tarihi.