NFF ta mayar da wasan Sierra Leone da Kwaddebuwa Fatakwal
Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ce ta mayar da wasan da kasashen Sierra Leone da na Kwaddebuwa za su yi na neman gurbi a gasar cin kofin Afirka daga Legas zuwa Fatakwal.Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta mayar da wasan Najeriya ne saboda yadda cutar Ebola ta yi wa kasar […]
Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ce ta mayar da wasan da kasashen Sierra Leone da na Kwaddebuwa za su yi na neman gurbi a gasar cin kofin Afirka daga Legas zuwa Fatakwal.
Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta mayar da wasan Najeriya ne saboda yadda cutar Ebola ta yi wa kasar Sierra Leone kamun kazar kuku al’amarin da ya sa aka dage kasar daga yin wasanninta na gida da hukumar ke shiryawa zuwa wadansu kasashe daban.
Da farko dai hukumar NFF ta ce za a yi wasan ne a filin wasa na Teslim Balogun da ke Legas amma daga baya ne ta yanke shawarar mayar da shi zuwa garin Fatakwal inda za a yi a filin wasa na Adokiye Amiesimaka.
Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Sierra Leone Augustin Sidy Diallo ya tabbatar ’yan kwallonsa za su sauka a Najeriya a yau Juma’a don tunkarar wasan. Wasan zai gudana ne da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya a tsakanin gobe Asabar ko a jibi Lahadi.
Wannan shi ne karo na farko da Najeriya ta karbi bakuncin wadansu kasashe don yin wasa a kasar.
Kafin Hukumar NFF ta amince ta karbi bakuncin wasan sai da ta nemi shawarar  Ma’aikatar kula da kiwon lafiya ta kasa gamne da yin wasan a Najeriya.