Bruno Labbadia: Muhimman abubuwa game da sabon kocin Super Eagles
Bruno Labbadia shi ne ɗan ƙasar Jamus da zai jagoranci horas da tawagar ’yan wasan Super Eagles na Najeriya.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) ta naɗa Bruno Labbadia ɗan ƙasar Jamus a matsayin sabon mai horas da tawagar ’yan wasan Super Eagles.
Sakataren NFF, Dr. Mohammed Sanusi, ya sanar a safiyar Talata cewa, “Naɗin Bruno Labbadia, a matsayin babban kocin ’yan wasan Super Eagles, ya fara aiki ne nan take bisa amincewar kwamitin gudanarwar NFF.”
Bruno Labbadia: Muhimman abubuwa kan sabon kocin Super Eagles
Bruno Labbadia ɗan shekaru 58, haifaffen yankin Darmstadt ne da ke ƙasar Jamus a ranar 8 ga watan Fabrairu, 1966.
Labbadia ya lashe gasanni sau biyu a ƙungiyar Die Mannschaft, kuma ya yi wasa a ƙungiyoyin Darmstadt 98, Hamburger SV, da kuma FC Kaiserslautern.
Ya kuma lashe gasanni da ƙungiyoyin Bayern Munich, FC Cologne, Werder Bremen, Armenia Bielefeld da kuma Karlsruher SC.
Ya kuma lashe gasar Bundesliga na ƙasar Jamus tare da ƙungiyar Bayern Munich a shekarar 1994.
Jagorancin ƙungiyoyi
Bruno Labbadia yana da lasisin kwararrun masu horas da ’yan wasa na ƙungiyar UEFA.
Ya kasance kocin kungiyar Hertha Berlin da VfB Stuttgart da VfL Wolfsburg, Hamburger SV, Bayer Leverkusen, a lokuta daban-daban.
Shi ne ɗan ƙasar Jamus na shida da zai jagoranci horas da tawagar Super Eagles bayan Karl-Heinz Marotzke, wanda ya jagoranci kungiyar sau biyu a shekarun 1970 da 1974.
Sauran su ne; Gottlieb Göller (1981), Manfred Höner (1988-1989), Berti Vogts (2007-2008) da kuma Gernot Rohr (2016-2021).
Höner ya jagoranci Super Eagles ta kai matsayi na biyu a Gasar Kasashen Afirka ta 1988, sai Rohr da ya kai ta Gasar Kofin Duniya a 2018 FIFA da kuma wasan ƙarshe na gasar a ƙasar Rasha.
Ƙalubalen da ke gaban Bruno Labbadia
Babban ƙalubalen da ke gaban Labbadia na farko shi ne sama wa Super Eagles gurbi a gasar AFCON 2025, ta hanyar lashe wasanninnsu da ƙasashen Jamhuriyar Benin ranar 7 ga Satumba a Uyo da kuma wasansu da ƙasar Rwanda a ranar 10 ga wata a birnin Kigali.
Akwai kuma wasu jerin wasannin samun gurbi guda huɗu da za a fafata a watannin Oktoba da Nuwamba.