NFF ta yafe wa ’yan kwallon Sunshine Stars da suka yi tsirara a filin kwallo

Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta bayar da umarnin a dage ’yan kwallon Sunshine Stars da ke Akure na Jihar Ondo su biyu watau Kunle Odunlami da Prince Aggrey bisa samunsu da laifin yin tsirara a lokacin da suke murnar jefa kwallo a raga. Hukumar shirya gasar firimiya ta Najeriya (LMC) ta ce […]

NFF ta yafe wa ’yan kwallon Sunshine Stars da suka yi tsirara a filin kwallo
NFF ta yafe wa ’yan kwallon Sunshine Stars da suka yi tsirara a filin kwallo

Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta bayar da umarnin a dage ’yan kwallon Sunshine Stars da ke Akure na Jihar Ondo su biyu watau Kunle Odunlami da Prince Aggrey bisa samunsu da laifin yin tsirara a lokacin da suke murnar jefa kwallo a raga.

Hukumar shirya gasar firimiya ta Najeriya (LMC) ta ce ta ci tarar kowanne daga cikin ’yan kwallon Naira dubu 50 don ya zama darasi ga saura a laifin yin tsira da suka yi a filin wasa saboda nasarar zura kwallo a raga.
Shi dai Odunlami, da ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles an same shi tare da abokinsa Aggrey ne da laifin tube rigunansu inda suka kasance daga su sai dan kamfai jim kadan bayan kulob dinsu ya zura kwallo ta biyu a ragar kulob din Dolphins ana gab da tashi wasa a gasar rukuni firimiya inda Sunshine ta samu nasara a wasan da ci 2-1 a ranar Lahadin da ta gabata.
Tuni Hukumar shirya gasar rukunin (LMC) ta bukaci ’yan kwallon su biya tarar ko kuma su daukaka kara a cikin awanni 48 idan ba su gamsu da hukuncin ba.
Sai dai ya zuwa jiya Alhamis hukumar ta bayyana cewa ta yafe wa ’yan kwallon a bias kuskuren da suka aikata na yin tsirara a filin kwallo bayan sun daukaka kara kuma sun rubuta takardar neman afuwa a kana bin da suka aikata. Hukumar ta ce ta gamsu da yadda ’yan kwallon suka nuna nadama da kuma yin alkwarin hakan ba za ta sake faruwa da sub a.