NFF tana tuhumar Stephen Keshi da bincent Enyeama
A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar shirya kwallon kafa a Najeriya (NFF) ta aika da takardar tuhuma (kuery) ga kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi da kuma golan kungiyar watau bincent Enyeama jim kadan bayan an gama wasan da Najeriya ta yi da Chad a Kaduna a ranar Asabar da […]

A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar shirya kwallon kafa a Najeriya (NFF) ta aika da takardar tuhuma (kuery) ga kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi da kuma golan kungiyar watau bincent Enyeama jim kadan bayan an gama wasan da Najeriya ta yi da Chad a Kaduna a ranar Asabar da ta gabata.
NFF ta ce tana tuhumar Keshi ne a kan ya yi mata bayanin dalilin da ya sa ya gayyaci wani dan kwallo mai suna Gabriel Okechukwu wanda ba a san shi ba, kuma ba ya buga wa wata babbar kungiyar kwallon kafa a ciki da wajen Najeriya kwallo, inda ya kasance daya daga cikin ’yan kwallon Eagles da ya zauna a benchi yana jiran ko ta kwana a wasan da bai kamata Najeriya ta yi sakaci da shi ba. Haka kuma hukumar ta ce abin mamaki shi ne yadda kocin ya ba dan kwallon fifiko wajen ba shi rigar wasa mai lamba 10 da ba kowane dan kwallo ne yakamata a bashi ba saboda muhimmancinta. Hukumar ta ce dan kwallon yana daga cikin ’yan kwallon da suka kasa kai batensu na hayewa gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na ’yan kasa da shekara 20 (U-20) da ke gudana a Newzeland a halin yanzu amma abin mamaki bayan an sallame shi daga cikin wadanda suka tafi gasar cin kofin duniyar sai Keshi gayyace shi Super Eagles ba tare da wani kwakkwaran dalili ba. Wadannan dalilai ne ta sa hukumar take tuhumar Keshi da ya yi mata bayani dalla-dalla na daukar dan kwallon ba tare da sanin hukumar ko amincewarta ba. Shi dai Gabriel Okechukwu yana buga wa wani kulob ne mai suna Water FC da ke Abuja da ke wasa a rukunin ’yan dagaji.
Shi kuma golan Najeriya bincent Enyeama, hukumar ta ce tana tuhumarsa ne a kan kalaman da ya yi a lokacin da hukumar ta yanke shawarar a yi wasan Najeriya da Chadi a garin Kaduna inda dan kwallon ya ce hakan bai dace ba saboda matsalar tsaro a Kaduna. Enyeama ya ce ya yi mamakin ganin yadda hukumar ta kai wasan Kaduna duk da matsalar tsaro da ta yi wa yankin Arewa katutu al’amarin da ya ce yin haka kuskure ne. Hakan ta tilasta wa shugaban Hukumar NFF Amaju Pinnick ya fitar da sanarwar babu abin da zai faru a Kaduna kuma hukumar ba ta da niyyar canza wasan zuwa wani gari daban.
Yanzu dai hukumar ta zuba ido ne ta ga irin amsoshin da kocin da kuma golan za su bayar a tuhumar da take musu.