NFF tana yunkurin sake daukar Stephen Keshi a matsayin Kocin Super Eagles

Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta ce ta fara yunkurin sake daukar Stephen Keshi a matsayin kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles don kawo karshen matsalar rashin takamaiman koci ga kungiyar a halin yanzu.Tun lokacin da aka kammala gasar cin kofin duniya a Brazil ne dai kwantaragin Keshi ya kare amma daga […]

NFF tana yunkurin sake daukar Stephen Keshi a matsayin Kocin Super Eagles
NFF tana yunkurin sake daukar Stephen Keshi a matsayin Kocin Super Eagles

Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta ce ta fara yunkurin sake daukar Stephen Keshi a matsayin kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles don kawo karshen matsalar rashin takamaiman koci ga kungiyar a halin yanzu.
Tun lokacin da aka kammala gasar cin kofin duniya a Brazil ne dai kwantaragin Keshi ya kare amma daga bisani sai Ministan matasa da wasanni Tammy Danagogo ya sake ba kocin dama don ganin ya haye da kungiyar zuwa gasar cin kofinAfirka amma abin ya faskara al’amarinda ya sa aka dakatar da kocin.
Sai dai kwamitin da ke kula da alhakin tantancewa da kuma daukar sabon koci a Hukumar NFF tuni ya zauna don duba yiwuwar sake daukar Kashi a matsayin kocin Super Eagles a shekaranjiya Laraba.&nbsp Wasu kafofin watsa labarai ma sun tabbatar cewa tuni kwamitin ya wanke Keshi kuma ya mika rahoto ga NFF don ta duba yiwuwar sake ba Keshi damar cigaba da horar da kungiyar ta Super Eagles.
Mataimakin Shugaban Kwamitin tantancewa da kuma daukar sabon koci a Hukumar NFF Alhaji Ahmed Yusuf Fresh ya tabbatar da cewa kwamitinsu ya zauna a shekaranjiya Laraba kuma babban batun da suka tattaunta shi ne na daukar sabon koci ga Super Eagles. &nbsp
Wata majiya ta ce akwai yiwuwar manyan jami’an gwamnati su tursasawa hukumar don ganin ta sake daukar Keshi a matsayin kocin kungiyar duk da cewa mafi yawa daga cikin ’yan Najeriya ba su son Keshi saboda rashin tabuka abin kirki da ya yi a baya musamman na kasa hayewa da Najeriya gasar cin kofin Afirka da aka kammala a kasar Ekuatorial Guinea a ranar Lahadin da ta gabata.