Ngige da ficewar likitoci kasashen waje
Yan Najeriya sun kadu sosai, a makon da jiya, yayin da aka ruwaito Ministan Kwadago da Inganta Ayyuka, Dokta Chris Ngige yana cewa Najeriya tana da rarar likitoci a kasa. Da ya bayyana a gidan talabijin, Ngige cewa ya yi ba ya ji ko a jikinsa kan yadda likitoci ke rububin barin kasar nan zuwa […]
Yan Najeriya sun kadu sosai, a makon da jiya, yayin da aka ruwaito Ministan Kwadago da Inganta Ayyuka, Dokta Chris Ngige yana cewa Najeriya tana da rarar likitoci a kasa. Da ya bayyana a gidan talabijin, Ngige cewa ya yi ba ya ji ko a jikinsa kan yadda likitoci ke rububin barin kasar nan zuwa ketare, don a cewarsa, Najeriyar tana da dimbin likitoci fiye da yadda ake da bukata. Sai dai daga baya ya kekasa kasa ya ce wai ba a fahimci bayanan nasa ba ne. Amma a martanin da Kunkiyar Likitocin ta Kasa (NMA), wadda ita ce uwar kungiyoyin likitocin kasar nan ta mayar, ta yi fatali da ikirarin Ministan, tana mai cewa; Najeriya tana fama da kamfar likitocin sosai, lamarin da ya sa jama’ar kasar nan ke fuskantar wahalhalu a sha’anin kiwon lafiya. Ngigen ya ce: “Ban damu ba, muna da rarar likitoci. Idan kuma muna da rara, sai kawai mu yi ta fitar da su ketare. Malaman da suka koya min darasin kimiyyar halittta (Biology) da na sinadarai (Chemistry) a sakandaren da na yi, Indiyawa ne. Sun kasance da rara, a kasarsu. Mu ma a halin yanzu, muna da rarar likitoci, ina mai tabbatar maka hakan. Saboda bangarena ne, muna da rara, fiye da yadda ake da bukata ka fada wa kowa ni na ce.” Shugaban Kungiyar NMA, Dokta Francis Faduyile, ya bayyana kalaman na Ministan, a matsayin wani abin takaici, yana cewa, “Ba gaskiya ba ne.” Faduyile, ya ce akwai alkaluman da ake amfani da su wajen tabbatar da ko kasa na da isassun likitoci ko a’a. Daya daga cikinsu a cewarsa, shi ne na dora mizanin yawan likitoci a kasa da yawan majinyata, bisa doron yadda Hukumar Lafiya ta Duniya, (WHO) ta kayyade, wanda ya nuna kowane likita guda ya lura da marasa lafiya 600 ne kawai. Amma a Najeriya, inji shugaban likitocin, kowane likita daya, yana duba lafiyar majinyata dubu biyar ne ko dubu shida. Ya kara da cewa, a wasu wuraren munin abin ya fi haka, inda za a samu likita daya yana lura da mutum fiye da dubu 10.” Ya kuma nuna cewa: “Ke nan yanzu a Najeriya hakan na gwada mana cikin majinyata dubu daya duka, muna fama da kamfar likita10. Don haka muna matukar fama da karancin likitoci.” A ce irin wadannan kalamai, na fitowa daga bakin Dokta Ngige, ba shakka babban abin kaico ne. Baya ga kasancewarsa Ministan Kwadago, wanda lallai ne ya san alkaluman likitocin da Najeriya ke da su, musamman ma a asibitocin gwamnati, wadanda akasari su ne suke fama da kamfar likitocin, kuma shi ma kansa likita ne lallai ne ya san halin da asibitocin kasar ke ciki da kuma irin bakar wahalar da marasa lafiya ke samun kansu a ciki, kafin likita ya duba su.
Bai kamata ya yi wannan subul-da-baka ba, kamata ya yi ya lura sosai da kamalan nasa, ya dora su bisa mizanin bayanai na hakika. Wannan ba shi ne karon farko da ake yin kalamai irin wadannan ba. A watan Satumban bara, an jiyo Ministan Lafiya Farfesa Isaac Folorunsho Adewole, yana cewa, ba lallai ba ne, a ce kowane likita, sai ya zama kwararre ba, don haka suna iya jarraba sa’arsu a wasu ayyukan na daban, kamar noma ko siyasa. Kalamai irin wadannan, sam ba su dace da jami’an gwamnati ba, domin suna nuni cewa, ita gwamnatin ba ta ma da masaniyar gaskiyar al’amarin da ke kasa.
Gaskiyar al’amarin da ke a kasa a halin yanzu a Najeriya dai shi ne batun da shugaban likitocin ya fada. In dai har gwamnati da gaske take yi, cewa ta inganta yanayin kiwon lafiya, to ya dace ta farga a kan har yanzu fa kasar na karancin likitoci, kuma lallai ne ta kara azamar kara yawansu. A wasu asibitocin ma, musamman ma a yankunan karkara a mafi yawan lokuta, za ka tarar da likita daya ne kacal, ko kuma babu ko guda ma a wasu wuraren. Sakamakon haka ne, ya sa da dama ’yan kasar nan suka gwammaci zuwa asibitoci masu zaman kansu wadanda sun fi karfin talaka.
A baya-bayan nan, an samu wadansu likitoci masu yawa, suna halartar ganawar neman aiki don yin aiki a asibitocin kasar Saudiyya. Lallai ne gwamnati ta yi kokarin kara inganta aikin likitoci, musamman ma kudaden da take ba su. Ta kuma kyautata wuraren aikinsu, tare da samar da dukkan kayayyakin aikin da suke bukata, domin hana su ficewa daga kasar nan.
Ministan ya ce, duk lokacin da likitocin suka yi hijira zuwa kasashen ketare, suna turo da kudade zuwa Najeriya, don haka ke nan, suna bayar da gudunmawa ta fuskar habaka tattalin arzikin kasa. Eh, hakan gaskiya ce, kuma ta wata fuskar abu ne mai kyau, amma ba hujja ba ce a bari suna tsallakawa zuwa waje. In da a ce, dukkan kwararrun likitocin da suka fice daga kasar nan, yanzu suna kasar, to da tabbas fita waje don neman lafiya ta ragu.