…Ngilari ya rantse, Fintiri ya ratse (2)
Lauyoyi sun ce hukuncin ya yi daidai Farfesa Auwalu Hamisu Yadudu, malamin fannin shari’a kuma masanin tsarin mulki, ya bayyana cewa hukuncin da kotun ta yanke shi ne ya dace da tanadin dake cikin kundin tsarin mulkin kasa.Ya ce, ‘’hukunci ba zance dacewa ba ne ko rashin dacewarsa, sai dai a ce ya yi daidai […]

Lauyoyi sun ce hukuncin ya yi daidai
Farfesa Auwalu Hamisu Yadudu, malamin fannin shari’a kuma masanin tsarin mulki, ya bayyana cewa hukuncin da kotun ta yanke shi ne ya dace da tanadin dake cikin kundin tsarin mulkin kasa.
Ya ce, ‘’hukunci ba zance dacewa ba ne ko rashin dacewarsa, sai dai a ce ya yi daidai da abin da kundin tsarin mulki ya yi tanadi ko doka? Abin da shi wannan mukaddashin gwamnan ya yi korafi a kansa shi ne, cewa da aka yi ya ajiye aiki an yi shi ne ba bisa ka’’ida ba, kuma yana ganin har yanzu shi ne mataimakin gwamna, kuma idan yana nan shugaban majalisa ba zai iya darewa kujerar gwmna da aka tsige ba. Kotu ta amince da abin da ya fada a bisa hujjar da ya bayar cewa tsarin mulki ya ce mataimakin gwamna zai iya cewa ya ajiye aiki, amma wanda zai bai wa takardar ajiye aiki shi ne gwamna, kuma ajiye aikin ba zai karbu ba har sai gwamna ya amince.’
“Sanin kowa ne ba a mika wa gwamna takardar ajiye aiki ba ballatana ya amince, kuma sanin kowa cewa ‘yan majalisa da suka fara yunkurin tsige su biyu, gwamna da mataimakinsa, sun yi azarbabi, inda suka dakatar da tsige shi mataimakin gwamna ko dai bisa shiri ko kuma bisa rashin sanin doka, sai suka tsige gwamna.”
Ya kara da cewa, “hakika wannanhukunci da kotu ta yanke, ni ba na ganin wani nkuskure a kansa, a kan cewa ba a tsige mataimakin gwamna ba, kuma bai ajiye aiki kamar yanda doka ta yi tanadi ba, saboda haka idan haka ne, har gobe shi ne mataimakin gwamna.”
Dangane da zaben cike gurbi day a kamata a yi gobe a jihar kuwa, sai Farfesa Yadudu ya ce “ hukuncin ya shafi zaben tun da shi shugaban majalisar dokokin ya hau kujerar ne saboda tsarin mulki ya bada dama idan babu gwamna, babu matamakinsa, ko kuma idan ba shugaban kasa kuma babu mataimakinsa, shugaban majalisa zai iya darewa kujerarsa, kuma za a yi zabe bayan kwana 90 da hawansa.”
Ya ce tun da yanzu kotu ta ce ba a samu gurbi ba a kujerar mataimakin gwamna ba don haka shugaban majalisa ba shi da damar ya dare kan kujerar gwamna. Saboda haka wannan darewa da ya yi ba ta yi daidai da doka ba, ba ta yi daidai da tsarin mulki ba. Saboda haka idan kotu ta ce ta dakatar da wannan zabe a bisa neman da wanda ya shigar da kara ya yi, daidai ne a dakatar da zabe, domin ko da an yi zaben kuma aka ce ko shi Fintiri ya ci ko wancan na APC ya ci, idan babu gurbin doka da za a yi zabe, idan an yi, an yi shi a banza ne.”
Ya bayar da misalin cewa an taba yin irin haka a jihar Anambra, a zaben shekarar 2011, a inda Andy Uba ya hau ana tababar cewa shi wancan mai sauka Peter Obi ko ya gama wa’adin mulkinsa ne ko bai gama ba? Wanda har bayan an yi zabe an ce Andy Uba ya ci zabe, ba a fi kwana 40 da hawansa karaga ba, kotu ta ce ai Peter Obi bai gama wa’adinsa ba a kan kujerar ba, saboda haka wannan zaben da aka yi ba shi da wani tushe. Ya ce haka shi ma wannan zaben idan an yi shi, ana iya samun baya da kura, irin waccan takaddamar ta taso kuma a soke zaben.
Ya kara da cewa, ‘’akwai tanadi iri uku game da hawan mataimakin gwamna bayan babu gwamna. Da akwai hawa na tsigewa, kamar wannan da ake ciki da hawa na mutuwar gwamna, akwai hawa na ajiye aikin gwamna. Ya ce ba shi da tabbas mai yiwuwa shi ma hawan tsigewa an yi masa tanadin kayyadaddun kwanaki kafin a yi zaben cike gurbi, kuma shi ma ba zai wuce wannan kwana 90 din ba. Ya ce saboda haka shi idan ya hau yanzu idan ka’ida ta kwana casa’in ta cika, shi ma lallai ne ya kira a yi zaben gwamnan da zai maye gurbinsa.
A game da cewarda wadansu ke yi cewa siyasar PDP ta sa aka yanke hukuncin haka don mulkin ya ci gaba da tabbata a hannun dan jam’iyyarta, shi ya sa aka dakatar da zabe, sai ya ce, “ai wannan kara da mataimakin gwamna ya kai ba PDP ce ta kai ba, duk da cewa shi dama bai fita daga PDP ba, amma ina tabbatar da cewa idan aka ci gaba da wannan tababa har lokacin da ya cancanta a yi zabe ya zo, ba a yi wannan zaben na wucin gadi ba, wani zai iya zuwa kotu ya ce ai kujerar da shi kansa mataimakin gwamnan yake kai wacce ya gaje ta, lokacinta ya kusa karewa. Kuma zai bukaci hukumar zabe ta shigar da wannan jihar a cikin tsarin jihohin da za a yi zabe na kasa gaba daya.”
Ya ce ko sauran jam’iyyu su yarda da hakan ko su ki yarda, ko ma me aka yi tanadin tsarin mulki zai bayyana kuma zai yi tasiri a nan gaba. Ya ce mataimakin gwamnan da zai hau yanzu ba zai iya kara kwana daya a kan kwanaki casa’in din da tsarin mulki ya tanadar masa ba, haka shi ma shugaban majalisa da aka sauke, idan ma har an bar masa ya ci gaba. Ya ce kada fa a mance shi ma shugaban zai iya daukaka kara ko ya nemi a dakatar da hukuncin da wannan kotun ta yi. Ya ce idan hakan ta faru kuwa kuma ya yi nasara, za a iya yin zaben nan a ranar Asabar din da aka tanada.
Shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa reshin jihar Taraba Mista Ibrahim Efioyum ya bayyana cewa hukuncin da kotun tarayya ta yanke cewa mukaddashin gwamnan jihar Adamawa Malam Umaru Fintiri ya sauka a rantsar da mataimakin Nyako Mista Bala Ngilari ya yi dadai.
Lauya Efioyam wanda masani ne a kan tsarin mulki ya ce wanann hukunci na bisa doka, domin kotun ta zartar da hunkucin ne kan cancantar karar da aka shigar a gabanta kuma tare da la’akari da sashin dokoki na kasar nan.
Kafin yanke wannan hunkucin gobe ne aka tsara gudanar da zaben cike gurbi gwamna a jihar ta Adamawa. Mukaddashin Gwamna Malam Umar Fintiri na cikin ‘yan takarar cika gurbi na Gwamna, kafin kotun ta bayar da umurnin ya bar ofis a rantsar da Mista Bala Ngilari a matsayin Gwamna.
Jama’ar jihar Adamawa wadanda suka bayyana ra’ayinsu dangane da wannan lamarin sun ce ba su yi mamakin hukuncin kotun ba. Malam Isiyaku Lawal ya ce bai kamata jama’ a suyi mamakin wanan hukunci ba domin ganin yadda al’amura ke faruwa a kasar nan.
Da yawa daga cikin mutanen jihar suna yi wa manyan Adamawa da suka tsaya kai da fata cewa sai an tsige Gwamna Murtala Nyako daga kujerarsa dariya. A cewar irin wadanan mutanen dama tsige Gwamna Murtala Nyako da wata manufa aka yi ta kuma manufar ta fito a fili yanzu.
Amma shi Malam Aliyu Yola cewa ya yi watakila ganin cewa jam’iyyar ta doshi faduwa a zaben da za a yi shi ya sa aka kai matsayin da ake a jihar a yanzu.
Ya ce shi Mukaddashin Gwamna Umaru Fintiri da hawansa ya maida hankalinsa ne waje raba kawunan jama’ar jihar ta hanyar kabilanci da addini wanda hakan ya sa an kusa a samu rikicin addini ajihar. Yace kila cire shi da kotu ta yi zai iya zama alheri ga jama’ar jihar.