Ngozi Iweala ta sake zama Shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya
An sake zaɓar Dokta Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin Shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya WTO a wani sabon wa’adin shekaru huɗu. Tsohuwar Ministar Kuɗin Najeriya za ta ci gaba da jagorantar ƙungiyar har zuwa 2029, yayin da sabon wa’adin zai fara ne daga ranar 1 ga watan Satumbar 2025 kamar yadda shafin yanar gizon WTO ya […]
An sake zaɓar Dokta Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin Shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya WTO a wani sabon wa’adin shekaru huɗu.
Tsohuwar Ministar Kuɗin Najeriya za ta ci gaba da jagorantar ƙungiyar har zuwa 2029, yayin da sabon wa’adin zai fara ne daga ranar 1 ga watan Satumbar 2025 kamar yadda shafin yanar gizon WTO ya wallafa a ranar Juma’a.
“Matakin ya nuna cikakken amincewa da jagorancinta na musamman da hangen nesanta na ci gaban WTO nan gaba,” a cewar shafin na WTO.
An fara aikin sake naɗin nata tun a ranar 8 ga Oktoba, 2024, wanda Jakada Petter Ølberg daga ƙasar Norway, wanda shi ne Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, ya jagoranta.
“Tunda babu wani karin dan takara da aka gabatar kafin wa’adin ranar 8 ga Nuwamba ya cika, Dr. Okonjo-Iweala ita ce kaɗai ta tsaya takara,” a cewa Majalisar Kolin kungiyar ta WTO.
“An gudanar da wannan mataki cikin tsari da gaskiya, daidai da dokokin WTO kan Tsare-tsaren Naɗin Daraktoci Janar mai lamba (WT/L/509).”
Dokta Okonjo-Iweala wacce ‘yar asalin Najeriya ce, ta fara wa’adinta na farko a ranar 1 ga watan Maris 2021.
Kazalika, ita ce mace ta farko kuma ‘yar Afirka ta farko da ta fara riƙe wannan muƙamin.