NHIS: Kotu ta ɗage bayar da belin Farfesa Yusuf zuwa 27 ga Fabrairu
Sai dai Farfesa Yusuf ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa.
Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa.
A ranar Laraba ne, Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Yusuf a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu.
A lokacin ne kotun za ta yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), na zargin Yusuf da karkatar da kuɗaɗen gwamnati lokacin da yake jagorancin NHIS a shekarar 2016.
Ana zargin ya amince da sayen mota kan kuɗi Naira miliyan 49.2 maimakon Naira miliyan 30 da aka ware a kasafin kuɗi.
Hakazalika, EFCC ta ce Yusuf ya bai wa gidauniyar GK Kanki Foundation kwangilar bayar da horo ta Naira miliyan 10.1ba tare da bin ƙa’ida ba, duk da cewa mutum 45 kaɗai aka horar maimakon 90 da aka bayyana.
Bugu da ƙari, ana tuhumarsa da bai wa kamfanin ɗan uwansa Hassan Yusuf, Lubekh Nigeria Limited kwangilar Naira miliyan 17.5, wadda ita ma aka ce ba bisa ƙa’ida aka yi ta ba.
Yusuf ya musanta duk zarge-zargen da ake yi masa.
A zaman kotun, lauya mai gabatar da ƙara, Francis Usani, ya buƙaci a hana belin Yusuf, inda ya ce bai cika sharuɗan belin da EFCC ta ba shi a baya ba, wanda ya haɗa da wajibcin kai kansa ofishin hukumar sau biyu a kowane mako.
Ya ƙara da cewa Yusuf ya yi fariya da dangantakarsa da masu ruwa da tsaki a siyasa, don haka akwai yiwuwar ya tsere idan aka bayar da belinsa.
Ya kuma bayyana cewa jami’an EFCC sun sha wahala kafin su kama shi tare da gurfanar da shi a kotu.
Sai dai lauyan Yusuf, O.I. Habeeb (SAN), ya roƙi kotu da ta bayar da belinsa, inda ya ce laifukan da ake zargin sa da suna da ikon samun beli bisa doka.