NHIS ta biya miliyan tara ga kwamitin binciken dakataccen shugaban hukumar

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano kwamitin da ministan lafiya ya kafa don bincikar dakataccen babban sakataren Hukumar Inshorar Lafiya, Farfesa Usman Yusuf ya karbi alawaus din zama na Naira miliyan 19 daga kudin inshorar lafiya da ma’aikatan da ke cikin tsarin suka biya. Takardun da Aminiya ta samu sun nuna cewa an […]

NHIS ta biya miliyan tara ga kwamitin binciken dakataccen shugaban hukumar

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano kwamitin da ministan lafiya ya kafa don bincikar dakataccen babban sakataren Hukumar Inshorar Lafiya, Farfesa Usman Yusuf ya karbi alawaus din zama na Naira miliyan 19 daga kudin inshorar lafiya da ma’aikatan da ke cikin tsarin suka biya.
Takardun da Aminiya ta samu sun nuna cewa an biya membobi 21 na kwamitin Naira miliyan 19 da dubu 184 daga asusun baidaya na hukumar NHIS a ranar 14 ga watan Satumban shekarar 2017 a zaman kwamitin ya yi na mako uku.
Bayanan biyan kudin sun nuna cewa kudin alawus ne na ’yan kwamitin binciken sannan kuma babbar sakatariyar ma’aikatar lafiya wacce har ila yau ita ce shugabar kwamitin, Hajiya Binta Adamu Bello ta karbi Naira miliyan daya da dubu 280. Sannan kowane daya daga cikin daraktoci 13 na kwamitin din ya karbi naira dubu 960 sai kuma mataimakan daraktoci da ke kwamitin kowanne ya karbi Naira dubu 640. Hatta masu kare lafiyar babbar sakatariyar kowanne ya karbi naira dubu 320.
Sakataren kwamitin, Dokta O.J. Amedu ya karbi Naira miliyan daya da dubu 900 kudin sayen takardun da kwamitin suka yi amfani da su.
 

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna