Ni ba aure ne a gabana ba – Jarumin Indiya Salman Khan
Jarumin fim din ‘Jai Ho’ Salman Khan ya ce shi a wannan lokacin, ba aure ne a gabansa ba.dan fim din ya nuna kosawa da yawan tambayar da ’yan jarida suke yi masa game da batun aure, inda har ya tsaro da hanyar wayancewa domin rage karsashin tambayoyin. A yayin da yake amsa tambayoyin ’yan […]

Jarumin fim din ‘Jai Ho’ Salman Khan ya ce shi a wannan lokacin, ba aure ne a gabansa ba.
dan fim din ya nuna kosawa da yawan tambayar da ’yan jarida suke yi masa game da batun aure, inda har ya tsaro da hanyar wayancewa domin rage karsashin tambayoyin. A yayin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida a kwanakin baya, ya ce shi fa saurayi ne gadagal a leda.
“Ni saurayi ne danye, wanda bai taba sanin wata diya mace ba kuma ina son ku san cewa ni ba aure ne a gabana ba, don haka babu wata budurwa da zan yi wa alkawarin aure a yanzu.” Inji Salman, a yayin da yake bayani a shirin talabijin mai taken ‘Koffee with Karan 4.’
Da aka tambaye shi cewa, to yaya zai yi da dimbin mata masoyansa da ke ta kokarin ganin sun ciwon kansa domin aure? Nan fa dan fim din ya ce: “Ba ni da wata sha’awa ga aure a yanzu kuma ba ni da shirin soyayya da kowace yarinya. A halin da nake ciki, ina sha’awar ci gaba da rayuwata ta samartaka.”
Salman ya ci gaba da bayaninsa da cewa: “A yanzu da nake da shekara 30 a duniya, ina jin dadin zaman samartaka. A yadda nake rayuwa, ina da zabin gudanar da abin da nake so ba tare da na yi wa wani bayani ba kuma ba sai na yi wa wata karya ba. Duk wadda ke son yin mu’amala da ni, kofata a bude take, ina maraba da ita, amma dai kada ta sanya tsammanin wani abu. A duk lokacin da na tashi yin aure, lokacin ne zan sadaukar da kaina ga budurwata. Ina daraja mata kuma zan ci gaba da daraja su. Babu wani lokaci da zan kaskantar da darajar mata ko in yi wani mugun kalami game da su.”