Ni ba maciyin amana ba ne – Edward Snowden (2)
Peter Taylor: Lokacin da ka kuduri aniyar bankado wadannan bayanan sirri, ka yi tunani kan abin da zai biyo bayan haka, na barin kasarka zuwa wata kasa, musamman ma ga shi ka tsinci kanka a kasar Rasha. Ka kuma yi tunanin hukumar Amurka da za ta sa ka a gaba da tuhuma, har sai ta […]
Peter Taylor: Lokacin da ka kuduri aniyar bankado wadannan bayanan sirri, ka yi tunani kan abin da zai biyo bayan haka, na barin kasarka zuwa wata kasa, musamman ma ga shi ka tsinci kanka a kasar Rasha. Ka kuma yi tunanin hukumar Amurka da za ta sa ka a gaba da tuhuma, har sai ta kama ka da laifi?
Snowden: Sosai kuwa…(ya fashe da dariya)
Peter Taylor: Dole ka yi wannan tunanin.
Snowden: Ban yi tunanin akwai wani mahalukin da ba zai yi tunani irin wannan ba (kafin ya aiwatar da wannan abin da na yi)…
Peter Taylor: …watakila ma har da zaman kaso na shekaru masu yawa. Ba ka yi tunanin hukumar Amurka ba za ta hakura ba, har sai ta kama ka? Na dai tabbata sai ka yi tunani irin wannan.
Snowden: Na fi damuwa da mummunan tasirin wannan tsari na hukuma ga al’ummar kasar Amurka baki daya, da yadda zai shafe su. Da yadda wasu za su fuskanci hadari mai girma. Abin da ya fi damuna ma shi ne, tunanin ta yaya za mu iya sanin abin da ya kamata mu sani a matsayinmu na ‘yan kasa, don mu kare kanmu (daga irin wannan leken asiri), da kuma yadda za mu iya bai wa al’umma kariya daga dabi’un gwamnati wajen satar bayanansu, musamman a wannan zamani na habbakar hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani.
Peter Taylor: Mece ce alakar da ke tsakanin hukumar tsaron Amurka ta NSA, da kuma kishiyarta ta kasar Birtaniya mai suna GCHk?
Snowden: Hanya mafi sauki da za a fahimci wannan alaka ita ce: ita hukumar GCHk tamkar wani reshe ne na hukumar NSA. Hukumar NSA na bai wa GCHk tallafi na miliyoyin daloli a duk shekara, tana ba ta kayayyakin aiki, da shawarwari, da kuma irin nau’ukan bayanan da za ta rika tatsowa. A nata bangaren kuwa, hukumar GCHk na bai wa hukumar NSA kafofin tatsar bayanan da take tarawa ne daga al’ummar kasar Birtaniya, da sauran kasashen da ita Birtaniyan take da ruwa da tsaki wajen tafiyar da su.
Peter Taylor: A duk fadin duniya ke nan?
Snowden: Eh, a duk fadin duniya. Wadannan bayanan sun hada da dukkan bayanan da GCHk ke tarawa cikin kasar Birtaniya. Amma abin mamaki, hukumar Amurka na riya cewa, wai ba ta musayar bayanai da kasar Birtaniya, amma a fili yake cewa suna yi.
Peter Taylor: Da hukumar NSA da GCHk suna cewa, “Eh mun yarda cewa muna tatsar bayanan jama’a masu dimbin yawa, amma kuma bayanan da muke bukata daga cikinsu kadan ne matuka. Ba ruwanmu da abin da mutane suke yi. Wadansu daidaiku ne cikin mutane muke nema.” Kuma idan ka dubi tsarin yadda suke tatso bayanan, za ka ga cewa, a hankali za su iya kaiwa ga wadanda suke nema, wato ‘yan ta’adda, da masu manyan laifuka, tare da masu safarar miyagun kwayoyi. To kuwa ka ga in haka ne, muddin suna son kama wadanda suke hari, dole ne su tatsi bayanai masu dimbin yawa, don ta haka ne za su iya kama wadanda suke nema.
Snowden: Eh to, mu ma kaddara abin da suka fada haka ne a zahirin rayuwa. Mu kaddara har wa yau suna tatsar bayanan dukkan jama’a….suna fa sanin duk abin da kake yi, da duk wuraren da kake zuwa…
Peter Taylor: To amma ai ba su bukatar irin wadannan bayanan…
Snowden: Eh na yarda ba su bukatar irin wadannan bayanan, na yarda suna amfani da bayanan ne a lokacin da wata babbar matsala ta taso. Wadannan dalilai na iya kama da hujjoji abin yarda, wadanda za su iya ba su damar amfani da Majalisar dokoki don samar da dokar da za ta halatta musu wannan aiki. To amma me ya hana su yunkurin samar da wadannan dokoki ta hanyar majalisa, don halatta musu aikin?
Peter Taylor: Da yawa cikin mutane a Birtaniya na iya cewa, “Eh, mun yarda gaskiya ne hukumar GCHk na tatsar bayanan mutane a sirrance, ba mu damu ba muddin hakan zai taimaka musu wajen gano miyagu cikin al’umma. Kuma bayan haka ma, mu mutanen kwarai ne, ba abin da za mu boye (wa hukuma).
Snowden: Mutane da yawa ba za su fadi haka ba. Kuma masu fadin waccan magana ba su yi kuskure ba, domin wannan wani lamari ne da za a iya yin muhawara a kansa. Amma tambayar da ta kamata a musu ita ce: shin, da gaske ne wannan tsari na leken asiri da hukuma ke yi ga ‘yan kasa, zai samar mana da tsaro? A kasar Amurka mun ga irin gagarumin leken asirin da hukuma ke gudanarwa kan jama’a, sama da shekaru 10 yanzu. Hukumar fadar “White House” ta nada wasu kwararru biyu don gudanar da bincike kan wannan tsari. Sakamakon da suka fitar shi ne, wannan tsari na leken asiri da tatsar bayanan jama’a bai da tasirin da zai iya hana ‘yan ta’adda kawo mana hari. Amfanin wannan tsari kadai shi ne don hada bayanan sirri. Amma inda matsalar take shi ne, sai a rika gaya wa al’ummar Amurka cewa, dalilin aiwatar da wannan tsari shi ne don kare kasa daga ta’addanci. Tabbas tsarin na da tasiri wajen hada bayanan sirri. Amma wannan ya sha bamban da a ce wai hakan wata hanya ce ta kariya ga kasa kai tsaye.
Peter Taylor: Daga cikin bayanan sirri da ka bankado akwai wani kundi da ke dauke da wani tsarin leken asiri mai suna: “Prism,” wanda a karkashinsa bayanai sun nuna irin alakar da ke tsakanin Gwamnatin Amurka da sauran kamfanonin sadarwa na sada zumunta da ke kasar, irin su Google, da Facebook, da kuma Yahoo! karkashin wannan tsari na “Prism,” hukuma ta tilasta wa wadannan kamfanoni na sadarwa ta hanyar doka, da su rika bai wa hukumar NSA bayanan sirri na jama’a, a duk sa’adda ta bukata daga gare su. Babbar manufar wannan tsari na “Prism” shi ne don bai wa hukuma gano ‘yan ta’adda da ke wajen kasar Amurka. Mene ne karin bayanin da za ka iya yi kan wannan tsari?
Snowden: Abin da wannan tsari na “Prism” ke nunawa shi ne, hukuma kan je kotu ne a boye, don neman damar aiwatar da kudurinta na tilasta wa wadannan kamfanoni. Wadannan kotunan jeka-na-yi-ka ne kawai. Kuma hukumar NSA na gaya musu ne cewa, “Muna neman bayanan wane da wane ne…” amma ba tare da bin ka’idar doka ba.
Peter Taylor: Babu wanda ya san hakikanin abin da ke faruwa ta bayan fage…
Snowden: Babu wanda ya san abin da ke faruwa, tabbas.
Peter Taylor:Wadanne irin nau’ukan bayanai ne hukumar NSA ke iya tatsa daga wayar salula irin ta zamani?
Snowden: Sunayen wadanda ka kira, da sakonnin tes da ka aika, da shafukan yanar Intanet da ka shiga, da dukkan lambobin wayar abokanka da ke cikin wayar, da wuraren da ka ziyarta a zahiri, da cibiyar siginar Intanet da ka yi amfani da su (Wireless Access Point) – a gidanka ne ko a ofis. Don haka, manhajar “Smurf Suite” wani hadakar tsarin tatsar bayanai ne daga wayar salula nau’in iPhone. Ita kuwa “Dreamy Suite” wata cibiya ce mai samar da makamashin lantarki, wadda aikinta shi ne ta kunna wayar salula ko ta kashe, ba tare da saninka ba.