Ni ba maciyin amana ba ne – Edward Snowden (4)

Peter Taylor:  Yanzu kana nufin ko da gwamnatin kasar Sin ce, ko ta Rasha suka bukaci hakan?Snowden:  Tabbas, sosai kuwa!  Domin muddin muka yarda cewa mun bai wa gwamnatin kasar Birtaniya wata kafa don tatsar bayanan sirrin jama’a don samun damar gano ‘yan ta’adda, to, Gwamnatin kasar Sin ma na iya gaya wa wadannan kamfanoni […]

Ni ba maciyin amana ba ne – Edward Snowden (4)
Ni ba maciyin amana ba ne – Edward Snowden (4)

 Edward SnowdenPeter Taylor:  Yanzu kana nufin ko da gwamnatin kasar Sin ce, ko ta Rasha suka bukaci hakan?
Snowden:  Tabbas, sosai kuwa!  Domin muddin muka yarda cewa mun bai wa gwamnatin kasar Birtaniya wata kafa don tatsar bayanan sirrin jama’a don samun damar gano ‘yan ta’adda, to, Gwamnatin kasar Sin ma na iya gaya wa wadannan kamfanoni cewa: “Muddin kuna son shigo da hajojinku cikin kasar Sin, to, dole ne mu ma ku ba mu irin wannan kafa don tatsar bayanan jama’arku.”
Peter Taylor:  Za ka iya tuna wannan hoton?  (Ya nuna masa wani hoto mai dauke da shi da wani tsohon Daraktan Hukumar CIA).
Snowden: (Ya tuntsire da dariya)
Peter Taylor:  Dole in tuna maka lokacin farin cikinka na baya.
Snowden:  Wannan shi ne Michael Hayden, tsohon Daraktan Hukumar CIA.
Peter Taylor:  Janar Michael Hayden ba ya cikin magoya bayanka.  Ga kuma abin da yake cewa: “Wannan shi ne tonon silili mafi girma da aka taba yi wa kasar Amurka a tarihinta gaba daya, a fannin leken asiri.  Kuma wannan ya mayar da agogon Hukumar NSA da kudurinta wajen aiwatar da ayyukanta, zuwa shekaru masu yawa a baya.”  Shin, ba ka ganin wannan zance nashi na nuna cewa kai maciyin amana ne?
Snowden:  Michael Hayden shi ne mutum na farko da ya fara bayar da umarnin a rika tatsar bayanan jama’a ta hanyar wayar salularsu a kasar Amurka.  Kuma wannan ya ci gaba har tsawon shekaru 10, kafin inzo in bankado wannan badakalar.  Wanda kuma wannan shi ne abin da ya tsayar da wannan tsari, ya kuma zama dalilin samar da wata doka da ta bai wa kowa kariya a kasar Amurka.  Tambaya a nan ita ce:  a madadin wa Michael Hayden ya yi waccan magana?  (Da ya ce ni maciyin amana ne) ban sayar da wadannan bayanai ba, ban kuma amfana da su ta kowace hanya ba.  Da yawa cikin mutane ma kan ce zaman gudun hijira ba karamin ci baya ba ne.
Peter Taylor:  To amma ai Michael Hayden na iya cewa, shi aikinsa (a matsayinsa na Daraktan CIA) shi ne ya bai wa al’ummar Amurka kariya da tsaro daga kowace irin cutarwa.  Abin da yake nunawa shi ne, abin da kai ka yi ya saba wa waccan manufa.  Domin sanadiyyar bankado wadannan bayanai, ka zubar wa dukkan Amurkawa da kimarsu a idon duniya.  Shin, wannan ba ya nuna cewa kai maciyin amana ne?
Snowden:  Ko kadan, ni ba maciyin amana bane.  Tambayar ita ce:  idan ni maciyin amana ne, to, amanar wa naci?  Domin bayanan da na debo na baiwa ‘yan jaridar kasar Amurka ne, da sauran kungiyoyin kare ‘yancin dan Adam.  In kuwa haka ne, to, wane ne hukuma take yi wa aiki?  Al’ummar Amurka suke yi wa aiki, ko sabanin haka?
Peter Taylor:  Mu dawo kan batun rayuwarka nan gaba.  Babban tsohon Lauyan Gwamnatin Amurka Eric Holder, ya ce akwai tsammanin sasantawa tsakaninka da Gwamnatin Amurka.  Shin, wannan wani abu ne mai yiwuwa?
Snowden:  Mun ga sauyi matuka daga bangaren gwamnati, tun shekarar 2013 lokacin da lamarin ya faru, inda a baya take ta zargina da cin amanar kasa da sauransu.  Yanzu mun daina jin irin wadannan zantuka.  Wannan ya sa nike fatan Gwamnatin Amurka za ta canza matsayinta kan abin da ya shafi tuhumar masu bankado badakala a kasar gaba daya.
Peter Taylor:  Yanzu kana nufin nan gaba idan bukata ta kama za ka iya zama da gwamnati don sasasanci ke nan?
Snowden: Sosai kuwa, me zai hana?  Na yi alkawarin ma ko fursuna zan iya yi.  Amma abin da bazan yarda dashi ba shi ne in zama wani zakaran gwajin dafi da gwamnati za ta yi amfani da shi wajen tsoratar da wadanda nan gaba za su ga badakala irin wannan, amma su kasa bayyanawa.
Peter Taylor:  Yanzu ko zaman kurkuru kana iya yi ke nan?
Snowden:  Sosai kuwa!
Peter Taylor:  Yanzu ba zai zama tufka da warwara ba, a ce kai da kake tutiyar rajin kare hakkin dan Adam da tabbatar da gaskiya, wai kaine a nan kasar Rasha, kasar da kowa ya san sunyi bakin suna wajen keta hakkin dan Adam?
Snowden:  Na rubuta bukatar mafakar siyasa a kasashe sama da 20, tun daga nahiyar Turai zuwa sauran nahiyoyi, amma kowannensu na shayin bani amsa, saboda tsoron kada su ce sun ki, ya zama kamar sun goyi bayan Gwamnatin Amurka.  Wanda wannan zai nuna wa mutanen su cewa, su ma suna iya toshe fadin albarkacin baki ke nan.  Ko kuma su ce sun amince, su samu matsala da Gwamnatin Amurka.  Amma duk da haka, na bayyana a fili karara cewa a shirye nike in koma Amurka.  Zan iya komawa kasar Amurka ko da gobe ne, muddin hukuma a shirye take ta kare mana ‘yancinmu.
Peter Taylor:  Yaya kake kallon mahangar Gwamnatin Amurka a yanzu?  Ma’ana, me kake tsammanin za su yi maka idan kace za ka koma gida?
Snowden:  To da farko dai sun ce idan na ce zan koma gida ba za su azabtar da ni ba.  Wannan dai na ji su ne kawai (ya fashe da dariya).  Amma duk da haka dai har yanzu babu wani cikakken tattaunawa tsakaninmu.
Peter Taylor:  Yaya take tafiyar da rayuwarka a nan?  Kuma daga ina kake samun kudin kashewa, musamman ganin dai dole ka ci abinci, ga kuma tufafin sa wa?  Daga ina kake samun kudin?
Snowden:  Alhamdulillah kam, ina da kudi.  Domin kafin in baro kasar Amurka, na yi ayyuka masu yawa da kwarewata, kuma na samu kudi mai dimbin yawa daga wannan aiki.  Kuma ina tare da su a halin yanzu.  
Peter Taylor:  Amma ta wace hanya kake iya cire wadannan kudi?
Snowden:  A’a, tsabar kudin ne tare da ni (ba a banki suke ba).
Peter Taylor:  Sun kai nawa?
Snowden:  A’a, ba zan iya fada ba, don hakan zai saba wa ka’idojin hukumar kwastam.
Peter Taylor:  Masu sauraronka daga nan Rasha na iya cewa:  daga dukkan alamu, zai yi wahala kasar Rasha ta baka mafaka ba tare da wata yarjejeniya ta karkashin kasa ba.  Haka ma hukumar tsaron kasar Rasha ta FSB, ba za su barka haka kawai ka shigo kasar ba tare da sun tatukeka da tambayoyi ba kan irin abubuwan da ka yi a baya.  Shin, akwai wani abu makamancin hakan?
Snowden: (Ya fashe da dariya) Haba dai, ko kadan.  Ka fa sani, na rusa rayuwata ce gaba daya, sanadiyyar bankado wannan badakala (don nemo ‘yancin jama’a), ta yaya kuma zan zagayo ta baya in ci gaba da yin abin da nayi adawa da shi a baya?
Peter Taylor:  To amma mu kaddara idan hukumar FSB ta zo ta ce tana son ka yi mata bayani kan abubuwan da ka yi a baya, da yadda ka yi su, (shin za ka yi musu bayani)?  Domin yanzu ka zama wani kamammen yaki ne a hannunsu, mai tsada.
Snowden:  Ai ba wani abu boyayye kan haka. Kuma duk abin da ka ga na bayyana daga cikin abin da na bankado, suna hannun ‘yan jaridar (Amurka da Birtaniya).  Ban shigo kasar nan da komai ba a hannuna.  
Peter Taylor:  To amma da ka shigo kasar, hukumar FSB sun zanta da kai?
Snowden:  Eh, sosai kuwa.  A filin saukar jirgi suka zanta da ni.  Kuma ban shigo kasar da komai ba.  Tun daga kasar Hong Kong na mika dukkan bayanan ga ‘yan jarida.  Na yi haka ne saboda na san zan shiga wata kasa ce inda bazan iya sarrafa bayanan ba muddin na shigo.
Peter Taylor:  To yanzu idan na ba ka kwamfutata, a matsayinka na kwararre wajen iya sarrafa kwamfuta, ba za ka iya kai wa zuwa ga wadancan bayanan da ka bankado ba?  Ko ba ka da wata sila da su yanzu?
Snowden: (Ya fashe da dariya) Ina, ko kadan ba zan iya ba.
Peter Taylor:  Ko a ma’adanar tafi-da-gidanka (Personal iCloud) ba ka da su?
Snowden:  Ko kadan, ban da su.  Wadancan bayanai da muke magana a kai, na mika su ga ‘yan jarida.  Kuma a halin yanzu an adana su ne a wata ma’adanar da ba ta jone da Intanet, wacce ake kira: “AirGas.”  Ba a jone da Intanet suke ba.  Manufar ita ce don a ba su kariya daga duk wani aikin leken asiri ko dandatsanci.  Hanya mafi sauki da za ka iya kare kanka daga irin wannan kutse na leken asiri shi ne ya zama ba ka hawa Intanet gaba daya.  Na san yadda ake adana sirri, har ya kubuta daga masu nemansa.
Peter Taylor:  Idan ka yi la’akari da dukkan abubuwan da suka faru, da kuma marhalar rayuwarka ta nan gaba, musamman ganin cewa ta yiwu kana iya yin zaman kaso na lokaci mai tsawo, shin, ka yi nadama kan abubuwan nan?
Snowden:  Nadamar da na yi ita ce na tsawon lokacin da na dauka kafin bankado wannan badakala.  Domin iya tsawon lokacin da ka dauka kana kallon irin wannan tsari na leken asiri da shiga hakkin jama’a na sirri, ba tare da ka yi wani abu ba, iya yadda tsarin ya dada munana da tabbatuwa.  Kuma wannan zai sa gyara kan matsalar ta zama mai matukar wahala.  Na dauki kaddara kan abin da ya faru, da irin hasarar da na yi.  Amma duk da haka, ina cikin kwanciyar hankali.  Ina kuma samun bacci a natse yanzu.
Peter Taylor:  Edward Snowden, ina godiya matuka.
Snowden:  Ni ma na gode.