‘Ni ba ’yar fashi ba ce amma na san mutanen da na sayi mota a hannunsu ’yan fa
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama wata mace mai suna Hauwa Mustapha da aka fi sani da ’Yar Borno bisa zarginta da laifin hadin baki da wasu mutum biyar inda suka yi fashi da makami a unguwar danbare da ke Kano.Wadanda ake zargi da fashin sun hada da Isa Sani da Sabi’u Abdullahi da […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama wata mace mai suna Hauwa Mustapha da aka fi sani da ’Yar Borno bisa zarginta da laifin hadin baki da wasu mutum biyar inda suka yi fashi da makami a unguwar danbare da ke Kano.
Wadanda ake zargi da fashin sun hada da Isa Sani da Sabi’u Abdullahi da Mohammed Yakubu da Hassan Mohammed da Bashir Sulaiman, kuma ana zarginsu da yi wa wani gida a unguwar danbare tsinke inda suka sace kayaan da suka hada da mota kirar Marsandi da wayoyin hannu uku da na’urar kwamfuta Laptop da talabijin da Naira dubu 147 da sauran kaya masu daraja.
’Yan sanda sun ce Hauwa Mustapha wacce ke zaune a Ring Road da ke Hotoro cikin birnin Kano ta dade tana taimakon ’yan fashi a jihar inda take ba su wurin buya da sauran kayan aiki.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano Ibrahim K. Idris ya ce matar ita ce ta bayar da hayar gidan da aka boye mahaifin shahararren dan kwallon kafar nan wato Mikel Obi wanda aka taba sacewa.
Sai dai yayin da take yi wa Aminiya bayani, Hauwa Mustapha ta tabbatar da cewa ita ce ta bayar da hayar gidan da aka boye mahaifin Mikel Obi haka kuma ta sayi mota daga hannun barayin, sai dai ta musanta cewa a cikin barayin take. “Na san cewa mutanen da na sayi mota a hannunsu ’yan fashi ne, sai dai ba kamar yadda ’yan sanda ke cewa ni ma daya daga cikin barayi nake ba. Ban taba gayyatar wasu barayi daga Jos ko Kaduna ko Katsina su zo su yi sata ba. Haka ma batun bayar da hayar gidan da aka boye mahaifin Mikel Obi, babu shakk ni na bayar da gidan amma ba tare da sanin hakikanin manufar abin da ’yan hayar za su yi da gidan ba. Ni dai na bar komai a hannun Allah, domin na san ranar Alkiyama na nan zuwa,” inji ta.