Ni ban ce zan rushe babban masallacin Abuja ba —Wike

Ya ce makiya da ‘yan adawa ne suka juya masa maganar shi

Ni ban ce zan rushe babban masallacin Abuja ba —Wike

Wike da babban masallacicin Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya karyata labarin da ake yadawa cewa yana shirin rushe wani sashe na Babban Masallacin Kasa da ke Abuja.

A maimakon haka, Ministan ya ce ya ba Shugaban Hukumar Raya Babban Birnin (FCDA) Injiniya Shehu Ahmed sa’o’i 24 ya yi masa jawabi a kan ainihin matsayin gwamnati kan rushe wani bangaren masallacin da kuma shirin biyan diyyarsa.

Hakan dai ya biyo bayan bukatar fadada aikin wata hanya da za ta wuce ta jikin masallacin, wanda hakan ya sa hukumomin shi suka nemi a biya diyyar shi.

Ministan dai ya bayar da umarnin ne lokacin da ya karbi jagororin kwamitin masallacin da ke karkashin Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, inda ya ce ofishinsa ba shi da niyyar kuntata wa wani addini.

Ya ce, “An ce wai na ba da umarnin rusa wani bangare na masallacin, amma wannan ba gaskiya ba ne. Makiya da ’yan adawa ne kawai suke son yin amfani da batun domin su bata min suna, wannan kuma ba sabon abu ba ne a siyasa.

“Ni da Sarkin Musulmi, wanda shi ne shugaban masallacin muna da kyakkyawar fahimta kuma ina girmama shi, kamar uba nake daukar shi. Duk abin da ya shafi masallacin kuma ina mutunta shi,” in ji Wike.

Ministan ya kuma tsaya kai da fata cewa ba shi da kudurin yin amfani da ayyukan shi don ya kuntata wa kowanne addini ko kabila, suna yi ne domin ci gaban birnin da ma Najeriya baki daya.

Daga nan sai ya bukaci jama’a da su guji yada kalaman da ba gaskiya ba musamman wadanda za su cusa kiyayya a zukatansu.