Ni da Babangida da AbdulSalami ba mu samu katin zabe ba – Gwamnan Neja
Gwamnan Jihar Neja, Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ya yi nuni da cewa rashin kyakkyawan tsarin rabon katin zabe da Hukumar zabe ta kasa ta yi, ya sanya shi da tsofaffin shugabannin kasar nan, wato Janar Babangida da AbdulSalami duk ba su samu katin zabensu ba.Gwamnan ya yi wannan kalamin ne a lokacin da ya gabatar […]
Gwamnan Jihar Neja, Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ya yi nuni da cewa rashin kyakkyawan tsarin rabon katin zabe da Hukumar zabe ta kasa ta yi, ya sanya shi da tsofaffin shugabannin kasar nan, wato Janar Babangida da AbdulSalami duk ba su samu katin zabensu ba.
Gwamnan ya yi wannan kalamin ne a lokacin da ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2015 a gaban majalisar Jiha da ke Minna.
Ya ce, “a daidai lokacin da nike yi muku jawabi, tsohon shugaban kasar nan Ibrahim Badamsai Babangida da Janar AbdulSalami Abubakar ba su karbi katin zabensu ba.”
Gwamnan ya bayyana wa ’yan majalisar cewa mafi yawan wadanda suka cancanci kada kuri’a ba za su damar yin zabe ba, a zaben shekara mai karatowa.
Da yake nuna takaicinsa kan yadda aka shirya tsarin rabon katunan, Gwmana Aliyu ya bayyana cewa, kananan hukumomi 11 ne daga cikin 25 na jihar suka samu kayan aiki, su ma tattare da matsaloli, inda ya yi nuni cewa a cikin kowane mutum 500 da suka cancanci kada kuri’a , mutum 12 ne kawai suka samu katin zabensu, a mafi yawancin rumfunan da ake raba katin.
Dokta Babangida Aliyu ya ce a mafi yawancin cibiyoyin da ake raba katin zaben, ko dai ka samu na’urar da aka kawo tana da matsala ko kuma ma’aikatan hukumar zaben sun bar aikinsu.
Don haka, ya yi kira ga Hukumar zaben ta INEC kan lallai ta jajirce wajen sauke nauyin da ya rataya a kanta, ta gyara wannan matsala da ake fama da ita, sannan ya ce, maimakon haka, kamata ya yi INEC ta kyale masu kada kuri’a su yiu amfani da tsohon katinsu, ta yadda ba za a tauye wa kowa hakkinsa ba.