Ni da Buhari tausaya mana za a yi ba murna ba – El-Rufa’i

Zababben Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya nemi ’yan Najariya su tausaya masa shi da zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari a maimakon taya su murnar cin zabe. Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana haka ne a lokacin da kungiyar Mazauna Jihar Kaduna (KAPA) da kungiyar Yarbawa mazauna jihar suka shirya masa addu’o’i na musamman […]

Ni da Buhari tausaya mana za a yi ba murna ba – El-Rufa’i
Ni da Buhari tausaya mana za a yi ba murna ba – El-Rufa’i

Zababben Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya nemi ’yan Najariya su tausaya masa shi da zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari a maimakon taya su murnar cin zabe.

Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana haka ne a lokacin da kungiyar Mazauna Jihar Kaduna (KAPA) da kungiyar Yarbawa mazauna jihar suka shirya masa addu’o’i na musamman a gidan Sardauna da ke Unguwar Sarki, Kaduna.
Ya ce, akwai bukatar ’yan kasa su kuma rika sanya su a cikin addu’o’insu domin samun nasara a mulkinsu. “Abin da ya sa nake ganin a daina taya mu murna shi ne domin za mu karbi mulki ne lokacin da tattalin arzikin kasar nan ya gama lalacewa,” inji shi.
Malam El-Rufa’i ya fada wa ’yan kungiyar ta KAPA cewa ana bin Jihar Kaduna bashin sama da Naira billiyan 90, kuma a cewarsa ga alama bashin zai haura Naira biliyan 100 kafin ranar 29 ga Mayu da zai karbi mulki daga hannun gwamnati mai ci.
“Idan mutane suka kirawo ni a waya ko suka zo domin taya ni murna ni da Janar Buhari nakan amsa musu da cewa na gode, amma abin da nake bukata a wajensu shi ne tausayawa da addu’a. Saboda ni da Buhari za mu karbi gwamnati ne da ke cike da bashi, abin ya lalace har gwamnatin Jonathan na fama da wahala wajen biyan albashi ma’aikatanta ta yadda sai ta karbo bashi domin biyan albashi,” inji shi.
Malam El-Rufa’i ya kara da cewa addu’o’in da kungiyoyin suka shirya musu shi ne ya dace domin hakan ne zai sa su samu nasara.
Ya ce gwamnatinsa ba za ta rika dibar kudin jama’a tana raba wa ’yan siyasa ba, komai matsayinsu a jihar. Ya kuma tabbatar wa ’yan kabilar da Yarbawa cewa gwamnatinsu za ta cigaba da gode musu bisa goyon baya da suka ba Shugaba Muhammadu Buhari har ta kai ga ya samu nasarar cin zaben da ya gabata.
A wani labarin kungiyar Katsinawa da Daurawa (KDK) mazauna Kaduna ta gudanar da addu’o’i na musamman ga zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin samun nasarar mulkinsa.
An yi addu’o’in ne a lokacin taron da kungiyar a karkashin jagorancin tsohon Sakatarenta kuma shugaban kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna Abuja, Alhaji Aliyu Bala Daura.
Alhaji Bala Daura ya yi kira ga Katsinawa da Daurawa a duk inda suke su ci gaba da bayar da irin tasu gudumawar wajen ci gaban kasar nan da sauran al’ummarta.
Ya ce ba komai ne za a bar wa gwamnati ba, wajibi ne a rika tallafa mata da addu’o’i da sadaukar da kai.
Kuma ya bukaci ’yan kungiyar su rika halartar tarukan kungiyar kuma su hada kai wajen ganin an yi zaben shugabannin kungiyar da ke zuwa cikin kwanciyar hankali.
“Wannan kungiyar na cikin mawuyacin hali na neman ta durkushe saboda rashin gudanar da zabe. Saboda haka muke kira a yi zaben lafiya,” inji shi.
Daga cikin ’yan kungiyar mazauna Kaduna da suka halarci taron akwai Alhaji Dauda Sulaiman Zangon Daura da Alhaji Mamman Mai’aduwa da Sadik Ahmad da Alhaji Salisu Usman da Alhaji Abdulhadi El-Ladan da sauransu.