Ni da fim mutu-ka-raba- Jarumi Abubakar
Wani fitaccen jarumin fina-finan Hausa a Jihar Legas mai suna AbubakarAbubakar ya ce shi da fim sai dai mutu-ka-raba, saboda ta yi masa komai a rayuwa.Jarumin wanda aka fi sani Abba KC ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Jihar Legas a makon jiya.Ya ce: “Na dauki harkar fim a matsayin […]
Wani fitaccen jarumin fina-finan Hausa a Jihar Legas mai suna Abubakar
Abubakar ya ce shi da fim sai dai mutu-ka-raba, saboda ta yi masa komai a rayuwa.
Jarumin wanda aka fi sani Abba KC ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Jihar Legas a makon jiya.
Ya ce: “Na dauki harkar fim a matsayin sana’a mai daraja, saboda na samu rufin asiri a cikinta. Kuma ba zan bar harkar fim ba har abada. Iyayen wata budurwata sun hana ni auren ta saboda ina fim, suka ce a wurinsu harkar fim ba sana’a ba ce. Amma ba su san cewa a harkar fim har gida na gina a Kano ba. Sana’ar fim ba abar rainawa ba ce. Ina shaida wa duniya cewa sana’ar fim ta daga darajata, ta hada ni da jama’a. Na fi ba sana’ar fim martaba fiye da komai a rayuwata.”
Ya ce iyayen budurwarsa sun manta arziki na Allah ne, duk harkar da kake yi komai kankantarta idan ya ga dama sai ya ba ka arziki a cikinta. Ba girman harka ba ne yake kawo kudi kuma ba kankantar harka ba ce ke kawo talauci.
“Na fara harkar da sayar da kaset a Legas a karkashin wani maigida, da haka har na bude shagona. Na fara fitowa a fim, har na zama jarumi, daga nan na zama darakta. Na kan je Kano da Kaduna da Abuja don yin fim.
Jarumin dan kimanin shekara 31 dan Jihar Kano ya shafe shekara bakwai yana sana’ar fim a Legas.
Ya fito a fina-finai kamar ‘MakashinKa’ da ‘Bayan Wuya’ da ‘Son Maso Wani’ da kuma ‘Tunani’, inda ya fi son fim din ‘Son Maso Wani’ saboda yana dauke da jigon soyayya.