Ni da kaina zan zabo magajina —Buhari ga gwamnoni

Buhari ya shaida wa gwamnoni da shugaban jam’iyyar cewa goyon bayansu kawai yake bukata

Ni da kaina zan zabo magajina —Buhari ga gwamnoni

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shaida wa gwamnonin jam’iyyarsa ta APC cewa shi da kansa zai zabi magajinsa a jam’iyyar a zaben 2023.

Buhari ya shaida musu cewa abin da yake bukata daga wurinsu shi ne goyon bayansu ga wanda ya zaba a matsayin magajin nasa a zaben 2023 da ke kara matsowa.

“Abin da nake bukata daga gare ku shi ne goyon bayanku a matsayinku na gwamnoni,” inji Shugaba Buhari.

Ya bayyana hakan ne a taron da ya yi da gwamnonin da kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, a Fadar Shugaban Kasa ranar Talata gabanin tafiyarsa zuwa kasar Spain domin halartar wani taro.

Tun da farko, Buhari ya bukaci gwamnonin da shugaban jam’iyyar da su tabbatar da hadin kai da dunkulewar jam’iyyar a wuri guda ta yadda za ta fitar da dan takarar shugaban kasa da kowa zai yi na’am da nagartarsa.

A cewarsa, ya kamata duk dan takarar shugaban kasar da jam’iyyar za ta fitar ya kasance mutum mai nagarta kuma mai kishin talakawa.

Sannan, ya zama wanda ’yan Najeriya suke so, kuma zai yi duk abin da da ya dace domin samun kaunar ’yan Najeriya bayan cin zaben na 2023.

Shugaban kasar ya ci gaba da cewa, “Shekarata ta karshe ke nan a wa’adin mulkina na biyu, saboda haka wajibi ne in mayar da hankali in jajircewa in tashi haikan domin tabbatar da ganin Jam’iyyar APC ba ta kauce hanya ba.

“Ba za mu bari gimshikan da aka assasa wannan jam’iyyar a kai su rushe ba, saboda haka ya zama wajibi mu hakura da juna mu yi abin da ya kamata.”

Don haka ya ce babban abin da jam’iyyar ta mayar da hankali a kai yanzu shi ne ganin yadda za ta yi nasara a zaben 2023.

Yin hakan, a cewarsa, na bukatar kowane bangare ya ajiye bukatarsa ya zo a hadu a yi abin da ya kamata domin ciyar da jam’iyyar ta APC gaba.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno