Ni dan banga ne ba dan fashi ba – Adamu Malam
A ranar Talatar da ta gabata ce Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ta gabatar da wasu ’yan fashi da makami da ta ce ta kama a kokarinta na kawar da batagari a cikin al’umma. Aminiya ta zanta da daya daga cikinsu mai suna Adamu Malam wanda ya ce shi dan banga ne ba dan fashi […]
A ranar Talatar da ta gabata ce Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ta gabatar da wasu ’yan fashi da makami da ta ce ta kama a kokarinta na kawar da batagari a cikin al’umma. Aminiya ta zanta da daya daga cikinsu mai suna Adamu Malam wanda ya ce shi dan banga ne ba dan fashi ba, sharri aka kulla masa:
Me ka yi aka kawo ka hedkwatar ’yan sanda cikin ankwa?
An kama ni ne da bindiga a hannuna, kuma bindigar na kwace ta ne daga wani dan fashi da na kama. Kuma na mika shi ga ’yan sandan Jere, amma sai na boye bindigar.
Me ya sa ka boye bindigar da ka kwace daga dan fashin?
Na aji ye ne kawai a wurina ba domin zan aikata wani abu da ita ba.
Ba ka da masaniyar cewa gwamnati ta hana rike bindiga ba tare da izini ba?
Rashin sani ya jawo min wannan abu. Ka ga yanzu ba zan sake ba domin kuwa ko gobe na sake kama barawo ko wuka ko sanda na samu a wurinsa zan mika ga jami’an tsaro.
Ke nan ba sayen bindigar ka yi ba?
A’a, ban saya ba, kamar yadda na fada maka, ni dan banga ne a can yankin Jere.
Yaya aka yi aka kama ka?
’Yan sanda ne suka kama ni bayan wasu mutane da ba mu san ko su wane ne ba sun buga wa wani dattijo a garinmu waya cewa ya kai musu kudi har sama da Naira dubu 500. Kuma suna ba ’yan uwanmu tsoro. Sai na nemo abokaina su biyu sai muka bi hanya da nufin zuwa kamo wadannan mutane, a kan hanyarmu sai muka hadu da ’yan sanda. Kuma kafin in tafi sai da na nemi DPO na Jere don sanar da shi, amma wayarsa na kashe. Na so in sanar da shi halin da ake ciki amma ban same shi ba.
Fadi gaskiyar yadda aka yi ka samu bindigar da ake zarginka a kanta?
A hannun wani barawo na karba a lokacin da yake satar mai. Sai na ji ihu suna bugun direban motar. Suna ganina sai suka yi harbi sai na fadi su kuma suna cikin motoci ne uku sai wasu suka shiga suka gudu, wasu kuma sun shiga daji. Da na ga sun shiga daji sai ni ma na bi gefen jikin jakin Babangida da ke kusa da wata gada tunda kusa ne da rafi. Sai na manne da gadar rike da sanda da takobina. Yana zuwa sai na buge shi da sanda. Yana faduwa sai na dauki bindigarsa yana kwance na ce da shi idan ya tashi zan harbe shi. Da na je na mika wa ’yan sanda shi sai ban ba su bindigar ba. Na san dai ba zai fada wa ’yan sanda yana rike da bindiga ba. Ni kuma ina ganin haka sai na ce ai na samu bindiga ke nan.
Wacce irin bindiga aka samu a wurinka?
karama ce fistol.
Kana nufin DPO na Jere ya san cewa kai dan banga ne?
Ya sani, domin na kwato shanun sata har kusan dari kuma idan na kama su ’yan sanda nake ba wa. Ko kuma in kirawo su su zo su karba. Babu abin da na sani sai aikin banga kuma barayi ko sun kai nawa ne ba na tsoronsu ko ban rike komai ba. Wallahi ko da duwatsu zan fada masu. Kuma in kore su idan kuma da kayan sata a hannunsu in karba. Da za ka je wurin da nake ka tambaya za su fada maka cewa gaskiya na gyara wannan wuri. Ko mota a da ba ka isa ka ajiye ba daga Tafa zuwa Jere ko dai a sace maka taya ko a janye maka man fetur, amma a yanzu sai motarka ta yi mako a wurin babu wanda zai taba ta. Kuma ni kadai ke wannan aiki sannan idan na kama sai in kira ’yan sanda in ba su.
Idan har kana taimaka wa ’yan sanda me ya sa suka kama ka da zargin fashi?
Abin da ya sa suka kama ni sun ce me ya sa ban mayar da waccan karamar bindiga da na karba a hannun barawon ba. Sun ce da na mayar da bindigar da babu komai.
Kai me ya sa ka boye bindigar?
Kuskure ne.
Tunda ka ce kana taimaka wa ’yan sanda kuma sun sanka me ya hana ka kira su ka fada masu halin da kake ciki a yanzu domin su kawo maka dauki?
Akwai lamboninsu a wurina, amma bari in fada maka gaskiya mun yi fada da wasu daga cikinsu a lokacin da aka sace shanun gidan gona sai na nemi su zo su taimaka mana suka ce su ba za su je ba, domin idan barayin suka hango fitilar motarsu za su harbe su. Sai na fada masu cewa tunda ba za ku taimaka ba ke nan ba ku da wani amfani a wurinmu. Tunda idan irin haka ya taso muka nemi ku taimaka mana ba za ku taimaka mana ba. Daga nan sai wani daga cikinsu ya ce sai sun yi maganina tunda na ce ba su da amfani. Kuma ina zuwa a ran nan daidai wajensu sai suka ce mu ’yan fashi ne. Kuma wallahi ba haka ba ne.
Shi wanda ka ce wasu sun buga wa waya ya kai kudi mene ne sunansa?
kanen Alhaji Nandu ne aka buga wa waya aka ce ya kai masu Naira dubu 500 ko kuma za a zo a kashe shi (Alhaji Nandu). Ni kuma sai muka tashi da nufin taimaka masa.
Ka sanar da Alhajin domin su kawo maku taimako?
Gaskiya bai san halin da muke ciki ba a yanzu. Yana kuma zaune ne a wajen Marabar Isa.
Ke nan kai ba dan fashi ba ne kamar yadda ake zarginka?
Sharri aka kulla min kuma laifin wadancan ’yan sandan ne da suka kama ni. Tunda ina zuwa wurinsu in zauna idan barayi sun zo hanya su bukaci in shiga mota mu je tare da su.
Yanzu yaya kake ji a ranka?
Ba na jin komai saboda ni na san ba sata na yi ba, kuma garin taimako ne hakan ya faru da ni saboda haka ba na jin komai a raina ba na kuma fargabar komai.