Ni matar manya ce ba ta yara ba —Rashida Maisa’a
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, Rashida Abdullahi wacce aka fi sani da Rashida Maisa’a ta ce ita fa ba matar yara ba ce, don haka yara su guji kawo mata hari cewa suna son ta da aure. Jarumar ta yi wannan bayani ne lokacin da take mayar da martani ga wani matashi da ya […]
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, Rashida Abdullahi wacce aka fi sani da Rashida Maisa’a ta ce ita fa ba matar yara ba ce, don haka yara su guji kawo mata hari cewa suna son ta da aure.
Jarumar ta yi wannan bayani ne lokacin da take mayar da martani ga wani matashi da ya yi wasu kalamai cewa zai aurem ta.
- Muna gyara tarbiyyar matasa ta hanyar hip hop —Nomiis Gee
- Bidiyon tsiraici ya janyo cire jaruma daga fim din Kwana Casa’in
A ’yan kwanakin nan wani saurayi mai suna Musa Rafinkuka ya wallafa hotunan jarumar tare da rubuta kalaman soyayya a shafinsa na Facebook cewa yana kaunar jarumar.
Ya rubuta cewa gimbiya sarautar mata da za ta amince to da ya yi wuf da ita.
Sai dai washegari sai ga matashin ya yi faifan bidiyo inda ya janye maganarsa tare da neman afuwar jarumar a kan kalaman da ya yi cewa yana son auren ta.
Matashin ya kara da cewa babu wanda ya yi masa barazana har ya fitar da faifan bidiyon.
“A gaskiya babu wanda ya yi mini barazana a kan abin da na yi.
“Da muka yi magana a waya ta nuna min bacin ranta.
“Nasiha kawai ta yi min cewa abin da na yi bai dace ba don haka na ga dacewar a nemi afuwarta ta wannan hanya da na bi na yi mata wannan abu,” inji shi.
Rashida Maisa’a ta bayyana cewa bayan da matashin ya yi wancan bayani sun yi magana da shi a waya inda ta nuna masa cewa ruwa ba sa’an kwando ba ne.
“Mun yi magana da shi wannan matashi wanda ya shaida min cewa ya kasance yana son fina-finaina tun yana karami.
“Ya rasa ta yadda zai yi sakonsa ya isa gare ni shi ya sa ya yi wannan magana.
“Na gaya masa cewa abin da ya yi bai kyauta ba.
“Babu abin da na gaya masa; na dai gaya masa cewa ni na kwana biyu ba yarinya ba ce.
“Ni matar manya ce ba ta yara ba. Ka kalli Maisa’a mana,” inji ta.