Ni na fara aikin rubuta littafin tarihin Shata – Ibrahim Sheme

A kwanakin baya ne marubuci kuma dan jarida, Ibrahim Sheme ya fitar da wani babban kundi da ke kunshe da tarihin shahararren mawakin Hausa, marigayi Mamman Shata Katsina. Aminiya ta gana da shi, inda ya warware zare da abawa na irin fadi-tashin da ya sha wajen samar da wannan littafi mai suna SHATA IKON ALLAH: […]

Ni na fara aikin rubuta littafin tarihin Shata – Ibrahim Sheme
Ni na fara aikin rubuta littafin tarihin Shata – Ibrahim Sheme

A kwanakin baya ne marubuci kuma dan jarida, Ibrahim Sheme ya fitar da wani babban kundi da ke kunshe da tarihin shahararren mawakin Hausa, marigayi Mamman Shata Katsina. Aminiya ta gana da shi, inda ya warware zare da abawa na irin fadi-tashin da ya sha wajen samar da wannan littafi mai suna SHATA IKON ALLAH:

 

Ko za ka bayyana yadda ka fara tunanin tunkarar rubutu game da marigayi Mamman Shata?

Da farko dai mahaifina ne ya fara hada ni da Alhaji Mamman Shata. Sun san juna matuka ta yadda zan iya cewa mutuminsa ne kwarai duk da yake bai yi masa waka ba. Mahaifina shi ya dauke ni ya kai ni wajen Shata, ya ce masa, “To ga danka.” Har Shatan ya yi ta mamakin cewa na girma haka. A lokacin, ban dade da gama jami’a ba. To ni kuma sai soyayyar Shata ta darsu a zuciyata, ya kasance a koyaushe ina so in je in gan shi. Don haka a duk lokacin da na samu sarari, nakan je in gaida shi a gida.

Ana cikin haka, ina aiki a Kaduna a matsayin Mataimakin Editan jaridar mako-mako ta Nasiha, sai na yi tunanin me zai hana a matsayina na marubuci in rubuta tarihin Shata? A lokacin, ba a damu da rubuta tarihin mawakan Hausa ba, an fi kokarin rubuta tarihin wadansu manyan mutanen irin ’yan siyasa da ma’aikatan gwamnati da ’yan kasuwa don a kira taron kaddamarwa a samu kudi. Ni kuma ina yi wa Shata wani irin kallo na fasihin mutum wanda ya kamata a taskace ayyukan da ya yi a rayuwarsa. Ni mutum ne mai yawan karance-karance, don haka na jima da ganin alfanun hakan a wasu al’ummomin. A karshe, sai na tafi Funtuwa na samu Alhaji Shata a gida, na fada masa niyyata, kuma ya amince da bukatata. A 1991 na fara aikin, kuma na fara yin hirar farko da shi.

Littafin da ku hudu kuka samar na farko mai suna SHATA IKON ALLAH, yaya al’amarin ya gudana kuma me ya biyo baya?

Ni dai na fara aikin a 1991, to har na yi shekaru da farawa sai Allah Ya hada ni da wani mutum mai suna Aliyu Ibrahim kankara. Bari ka ji yadda abin ya faru, daga 1991 din nan har zuwa 1996 na dan yi abubuwa bakin gwargwado. A 1992 na bar jaridar Nasiha, na zama Editan Mujallar Rana (ta Kamfanin Hotline). A 1993 na tafi kasar Birtaniya domin yin digiri na biyu a Jami’ar Cardiff. Da na dawo, na dan yi aiki a matsayin Editan Mujallar Hotline kafin in koma jaridar New Nigerian, inda har na yi Mataimakin Edita.

Duk a tsawon wannan lokaci ban daina aiki kan tarihin Shata ba. A daidai lokacin ina da wani aboki mai suna Ibrahim Malumfashi, wanda malami ne a Jami’ar Usman danfodiyo a Sakkwato, yanzu kuma Farfesa ne a Jami’ar Jihar Kaduna. Wata rana, ina jin a 1997 ne, sai ya zo har gidana ya ce mini akwai wani mutum da ya ce masa yana so ya gan ni kan aikin rubuta tarihin Shata. Ya ce mini mutumin ya ce shi ma yana rubuta tarihin Shata kuma yana so mu hade mu yi littafi daya. Ya ce sunan mutumin Aliyu Ibrahim kankara, wanda malami ne a Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Kaduna (Kaduna Polytechnic).

Kamar ba zan amince ba, amma Malumfashi ya ja hankalina kan cewa mu dai hadu da wancan din, inji da wacce ya zo, kafin in yanke shawara. Sai na ce to shi ke nan, su zo tare, in ga abin da shi kankara ya rubuta.

Washegari, suka zo gidana, kankara ya zo da littafi, inda ya yi rubutu mai yawa da biro. Na karba na shiga dubawa sai na lura da cewa kankara na da irin azamar da nake bukata, kuma har ya yi hira da wadansu mutanen da Shata ya yi wa waka, wadanda ina so in yi hira da su. A lokacin ni ma fa na yi hirarraki da mutane da dama, wadanda shi bai kai gare su ba, irin su Indon Musawa da Shehu Maigidaje da Goshin dangude da Amadu Doka da Garban Bichi da dangin Shata a Musawa da sauransu. To, sai na ga lallai hadewarmu za ta taimaki dukanmu; ka ga ai ba sai na tafi wajen wadancan mutanen da ya yi hira da su ba, shi ma ba sai ya je wurin wadanda na yi hira da su ba. Saboda haka nan take na ce na yarda mu yi littafi daya. Babban dalilina shi ne, ni ba domin in samu kudi nake yin aikin ba. Burina dai in cimma nasarar tattara tarihin Shata, saboda haka ko wane ne ya zo ya ce mu hadu mu kai gaci zan amince.

A nan kankara ya bar mini wannan rubutu da ya yi, a matsayina in jagoranci aikin. Haka kuma, bayan wani lokaci, na dauke shi a motata, na kai shi wajen Shata a Funtuwa na ce, “Baba, wannan shi ne wane, yanzu da shi muke rubuta tarihinka, yana taimaka mini.” Shata ya ce to ba komai tunda ni na yarda da hakan.

To, daga nan fa sai muka bazama aiki, shi ya yi nan, ni in yi can, wani lokacin mu tafi waje tare. Da yake aikin tattara tarihin Shata kamar teku ne, sai dai ka debi na diba ka bar sauran, haka mu ka rika tafi da aikin bakin iyawarmu. 

Ina so ka sani cewa babu wata kungiya ko wani mutum da suka dauki nauyinmu kan wannan aiki; ni ne ke daukar nauyin yawancin aikin, da yake bakin gwargwado na fi kankara samu. Duk inda za mu, ni ke daukar nauyinmu. Haka nakan tura kankara wasu wuraren, in ba shi kudin zuwa da dawowa. Misali, na tura shi Bauchi ya yiwo mana hira da Garkuwan Bauchi Alhaji Ahmadun Kari, na tura shi Gombe ya yi mana hira da Garkuwan Gombe Alhaji Bappa Ahmed, wanda Shata ya yi wa wakar “dan Liman Uban Ciroma, dan Shehu Garkuwa.” Na tura shi Musawa ya wo mana hira da Magajin Gari Abdullahi Inde da su Ayuba Mainama da sauransu. Ya kamata ka sani, ni ma fa ba a kwance nake ba, ina nawa rangadin. Kuma dai ni ne ke zuwa wajen Shata a kai-a kai, ina sanar da shi halin da ake ciki.

Ana cikin haka, ran nan na je wajen Shata sai ya sanar da ni cewa wadansu mutum biyu sun same shi a Kabo Guest Inn a Kano, wato otal din Jarman Kano Alhaji Muhammadu Adamu dankabo, sun fada masa cewa suna rubuta tarihin rayuwarsa. Ya ce mini, “ka san su?” Na ce ban san su ba. Sai nan take wadansu yaran Shata da nake da matukar kusanci da su, irin su Alhaji Ya’u Wazirin Shata, suka ce ai kuwa ya kamata a kira su nan Funtuwa, a hana su ci gaba da aikin, domin dai ni aka sani, ni aka amince mawa. 

Shata ya yarda, ya ce to yaya za a yi a gano su? Na ce ina da abokai marubuta a Kano, zan iya zuwa in gano su. Aka sa ranar da za a ce su zo Funtuwa mu hadu mu duka idan na gano su. Daga Funtuwa na ja mota ban zame ko’ina ba sai Kano. Ta hanyar wani abokina marubuci, Ado Ahmad Gidan Dabino, na shiga bincike har aka kai ni wani gida a Unguwar Daneji, aka ce nan ne gidan su Ali Malami, wato daya daga cikin wadanda aka samu labarin suna aiki kan tarihin Shata. Na yi masa sallama, ya fito. Da muka tattauna, ya tabbatar mini da cewa lallai shi da wani mai suna Yusuf Tijjani Albasu sun fara rubuta tarihin Shata. Na isar da sakon cewa to Shata na nemansu a Funtuwa a rana kaza. Ya ce to insha Allah za su je. Ban fada masa matsayina a wajen rubuta tarihin Shata ba.

Daga Kano, sai na zarce zuwa gida Kaduna,na samu Aliyu na fada masa abin da ake ciki. Da ranar ta zo, muka rankaya zuwa Funtuwa – ni da kankara da wani abokina da na dauka a Zariya, wato Yahaya Umar. Muka yi sa’a, Alhaji Shata bai je ko’ina ba. Da ya fito zaure ya zauna, aka taru kamar kullum, ana jirar isowar Kanawan nan. Can kuwa sai ga su sun iso tare da wani abokinsu kuma sun zo da littafinsu kamar yadda aka ce su yi. Abin da aka shirya shi ne, idan sun zo, za a kwace littafin ne, a kore su bisa hujjar cewa Shata bai ba su izinin rubuta tarihin rayuwarsa ba! To amma sai na ce a ba ni dama in duba aikin da suka yi. Su duk ba su san shirin da aka yi ba.

Na karbi littafi biyu da suka cika da rubutu da biro, muka koma waje, na jingina da mota na shiga dubawa. Littafi daya na kunshe da matanonin wasu wakokin Shata, yayin da dayan – wanda shi ya fi jan hankalina, yana dauke da hirarraki da wasdanu mutane da Shata ya yi wa waka. Kamar dai yadda na gano lokacin hadewa ta da kankara, sai na ga cewa lallai Kanawan nan sun yi aiki irin wanda nake so; sun yi hira da wadansu mutane wadanda muke da burin ganawa da su, irin su Delun Kunya da Abubakar Uwawu da Umaru danduna da Liman ’Yalleman da Laila Dogonyaro da sauransu.

Da muka koma gaban Shata, sai na ce masa, “Baba, ni ina ganin ya kamata mu hade da wadannan su ma, a yi littafi daya.” Sai mamaki ya kama kowa. Shata ya ce, “Haka kake so?” Na ce, “Eh.” Ya ce, “To ai shi ke nan.” Sai na ba da shawarar mu koma waje mu tattauna tare da Ali Malami da Yusuf Tijjani Albasu. Da muka koma, na fada musu irin aikin da muka yi kuma na nuna musu namu aikin tare da dimbin hotunan da muka tara. Nan take su ma suka amince cewa mu hade mu hudu mu yi littafi daya.

Bayan mun tattauna, na rubuta takardar yarjejeniya, muka koma gaban Shata, na karanta ta kowa ya ji. Aka amince, kowa ya rattaba hannu a kan cewa mun hade.

Daga nan, aiki ya koma danye. A matsayina na jagoran aikin, na kira taro a Kaduna, inda muka tattauna kan yadda aikin zai kasance, musamman abin da ya rage mana da kuma yadda za a yi mu ci gaba da tunkarar aikin. Kowannenmu zai ci gaba da bincike kamar yadda muka faro, sannan ni ne marubucin littafin, wato ni ne zan karanta abin da kowannen mu ya farauto, in saka shi cikin sassan littafin kamar yadda na tsara shi.

A tsawon lokacin da muka yi, na lura da wani abu. Abokan aikina sun damu matuka kan lallai in gama littafi a kaddamar da shi. Ni kuma ga ni aiki nake ta yi, har yanzu ban samu kaiwa inda nake so littafin ya kai ba. kullum gani nake yi akwai gibi nan da can. Ana haka har Shata ya fara ciwon ajali, ya koma ga Mahaliccinsa. A karshe, littafin bai fito ba sai a cikin shekarar 2006, wato shekara bakwai bayan rasuwar Shata.

 

Za mu ci gaba