Ni na sa a koma da hedkwatar Najeriya Abuja – Janar Gowon

A kwanan baya ne sashin Hausa na Muryar Amurka ya yi hira da tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon kan al’amura daban-daban, Wakilin Aminiya da ke Washington ya aiko da cikakkiyar hirar kamar haka: Aminiya:Ka san Buhari kuma dukkanku kun yi shugabancin kasar nan, yanzu ga shi ya sa farar riga zai mulki kasar nan, […]

Ni na sa a koma da hedkwatar Najeriya Abuja – Janar Gowon

A kwanan baya ne sashin Hausa na Muryar Amurka ya yi hira da tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon kan al’amura daban-daban, Wakilin Aminiya da ke Washington ya aiko da cikakkiyar hirar kamar haka:

Aminiya:Ka san Buhari kuma dukkanku kun yi shugabancin kasar nan, yanzu ga shi ya sa farar riga zai mulki kasar nan, yaya kake ganin zai yi wannan aiki na shugabanci cikin farin kaya?

Gowon:Misali ni lokacina, duk da yake ina cikin kayan soja ne, yawancin abubuwan da nake yi nakan tambayi jama’a su ba ni shawara, da dai sauransu. Duk da yake muna sanye da kayan soja muna aiki kamar na demokaradiyya a wannan lokacin,sai dai mu babu batun zabe, amma mukan nemi shawarar jama’a ta hanyoyi daban-daban, ko ta jarida, ko ta rediyo, ko irin wadannan tambayoyin da kuke yi a yanzu. Mukan ji shawarar da ake bayarwa kuma muna anfani da su, kusan kodayaushe saboda zaman lafiya.
Aminiya:To yaya kake ganin Buhari zaiyi mulkin a matsayin farar hula?
Gowon: Shi Buhari na sanshi tun kafin ya zama shugaban kasa na soja, domin ya yi aiki tare da ni, yaro ne(dariya), sabo da na ba shi wajen shekara 6 zuwa 7, ina sonsa kwarai da gaske, domin yana da gaskiya yana sanya gaskiya ga duk aikinsa kwarai da gaske, kuma akwai shi da kokari a duk aikinsa.Saboda irin gaskiyar da sanshi da ita, na taba ba shi aiki a cikin aikin soja wanda ya fi karfin mukaminsa a wannan lokacin, kuma ya yi yadda ake so.Don haka ni kam zai samu cikkakken goyon bayana, kuma ina kira ga sauran tsoffinn shugabannin kasa da su ba shi dukkan goyon bayan da yake bukata, domin mutum ne mai gaskiya kuma kowa ya san da hakan.Yakamata duk tsohon shugaban kasan da ke da shawarar da zai bayar ya je ya same shi ya fada masa, ba wai a rubuta a jaridu ba, ko kuma a rika fadi a radiyo ko talabijin ba, saboda kawai a bata wa shi shugaban kasa suna.
Aminiya:Ranka ya dade Buhari ya karbi mulkin kasar nan ba kudi ba mai, ba ruwa, ba wuta, ga basussuka a kan kasar, yaya kake ganin zai yi mulkin kasar nan?
Gowon:Duk wannan batu ne irin naku na ‘yan jarida.
Aminiya: Amma ai gaskiya ne babu wadannan abubuwan?
Gowon:Ko lokacinmu wadanne irin karerayi ne ba a yi ba a kaina? kuma ga shi a lokacin sun ce wai ba a yi wani abu ba, lokacin mun kare tsara shirin abubuwan da za mu yi (DEbELOPMENT PLAN) na shekarun 1975-80, a lokacin wa ya san inda wannan shirin zai kai Najeriya? amma ba an zo an ce wai ba mu yi wani abu ba? to ai irin wannan ne, ku rika yi a hankali.
Aminiya: Game da batun tallafin nan na mai, me yakamata a yi, a barshi ko cire?
Gowon:Yakamata bisa gaskiya a cire shi, saboda zambar da ake yi a kan sa zai fito, saboda mu ga ko mene ne yakamata a biya sai mu biya kan gaskiya, domin za mu iya biya.
Aminiya: Lokacin mulkinka wasu sun ce ka ce matsalar Najeriya ba kudi ba ne, yadda za ta kasha kudin ne, ranka ya dade wai ka taba yin wannan maganar kuwa?
Gowon:Abin da ‘yan jarida suke fadi shi ne, muna barna da kudi ne kawai, ba wai kudin da ake da shi ba, amma wane irin amfani ne kudin zai yi wa Najeriya domin a gyara sha’anin tattalin arzikin kasa da kuma jin dadi da biyan bukatun jama’a, wadanda suka taimake mu domin a rike kasar nan yadda ya kamata. Gaskiya ne yakamata a sake duba wannan batu na tallafi domin zai sa mu gane zambar da ake yi kuma mu san mene ne yakamata mu biya su masu kawo mana mai din. Ka ga a lokacin da na bari kamfanonin mai irin su Shell da BP da Mobil da sauransu, idan na barsu a ce ‘yan kasa su ma su yi nasu, watakila za mu rika samun gaskiya cikin wannan abin da ake yi.
Aminiya:Ana cewa Najeriya ta fi kowace kasa a Afrika arziki, amma ba a ganin arzikin a wurin talakawa, me ya sa?
Gowon:Wane irin ba a gani a wurin talakawa?
Aminiya:Ranka ya dade ba a gani a jikin talaka
Gowon:Don Allah a daina irin wannan maganar, fadi ne dai kawai ake yi domin a bata wa Najeriya suna, mutane suna amfana. Idan ma akwai rashin aikin yi cikin ‘yan samari da sauransu, wace kasa ce ba ta da wannan matsalar, ko a Amurka ba su da wannan wahalar ne? muna gani a talabijin ko yaushe a CNN da sauransu.
Aminiya:Amma ranka ya dade ko yaushe a ce babu abubuwan jin dadin rayuwa?
Gowon:Babu wuta, wannan shi ne nake fada maka, lokacin gwamnatin da suka tunbuke ni daga mulki me ya sa ba su ci gaba da kokarin da muka yi ba? Lokacin Sir Abubakar TafawaBalewa shi ne ya fara aikin lantarki na Kainji , amma mune muka karasa aikin lokacin da Allah Ya yi masa rasuwa. Nine na kunna babbar wuta na Kainji wadda ta ba mu isasshen wutar da za ta kara inganta ayyuka da rayuwar mutanen kasa
Aminiya: Amma lokacin da kake mulki ba za a kwatanta yawan wutar da Najeriya ke amfani da ita da yanzu ba.
Gowon:Wannan gaskiya ne, abin da ya faru shi ne, mun ce za a inganta wutar da yin wani aiki a Jebba da wani a Shiroro, za mu kuma yi wani a can Gembu-Manbila, kuma muna so mu yi amfani da wutar da ake konawa a wajen samar da fetur don samun isasshen wuta saboda a kara samun isasshiyar wutar da za ta taimaka mana aiwatar da shirinmu (DEbELOPMENT PLAN) da muka yi.Ba na gwamnatin tarayya kadai ba ce, duk da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi, amma gwamnatin da karbi mulki daga hannunmu ba ta yi wannan ba, sai aka yi ta zargi na, a ce wai saboda ban yi wannan ba ne, ban yi wancan ba.
Aminiya:Ana zarginka da cewa ka fi samar da aikin ci gaba a Legas fiye da Arewa, ka ji wannan zargin?
Gowon:Shi ya sa nake fada maka idan da a ce an bi shawarar da muka tsara, irin gyare-gyaren da za mu yi a cikin Najeriya baki daya wannan daban ne, batun gyara Legas kuwa ai a wancan lokacin shi ne babban birnin kasarmu kuma dole ne a gyara shi, domin abin da yakamata ke nan, ita Abujan wane ne ya sa aka soma Abujan? Nine, domin irin wahalar da aka samu bayan yakin basasa muka ce yakamata mu samu wurin da za mu iya kare shi daidai yadda yakamata, ba kamar Legas ba, muka ce mu bar Legas ya zama babbar cibiyar kasuwanci, ita kuma Abuja ta zamo birnin tafiyar da mulki, muka ce a samu tsakiyar kasa, wannan ne ya sa na zagaya jihohi irin su Binuwai da Filato da Kaduna da wadansu sassan Arewa Ta Tsakiya da Arewa Maso Yamma, wato jihohin Sakkwato Ke nan da Neja a lokacin, domin in ga inda za a samu wannan wurin. Mun soma daga can Gidan waya da Kafanchan da Wamba, zuwa wurin su Godi zuwa Keffi, na zo har nan Abuja a cikin jirgi mai saukar ungulu, ni da gwamna Gomwalk na tsohuwar jihar Binuwa-Filato, muka tashi kuma muka zagaya muka yi kamar za mu tafi Ilorin, muka kara zuwa Abaji har zuwa Toto, zuwa Nassarawa, kana muka koma Keffi. Bayan da na gama zagayawa na dudduba na gani, to wurin da na ga ya fi kyau shi ne wannan wurin tsakanin Keffi da Abuja wato Suleja da Abaji da Toto da Nasarawa, amma na ce kada a gina shi kusa da manyan garuruwa kamar su Keffi da Nasarawa da Abuja, abin da ya faru Ke nan.To amma Allah bai sa na karasa wannan ba, amma na fada wa duk wadanda suke tare da ni, wato Majalisar zartarwa (Fedral Edecutibe Council) da Majalisar koli ta mulkin soja (Supreme Military Council), da manyan hafsoshin soja cewa ga inda za a yi wannan babban birnin.
Aminiya:Ko da ka bar mulki Najeriya tana da jihohi 12, yau tana da 36, amma har yanzu wadansu na cewa a kara, yaya kake kallon wannan maganar?
Gowon:Na soma da 12, amma Najeriya ta soma da 3 ne, Tafawa balewa ya zo ya kara daya, ni da na zo saboda abin da Ujukwu ya yi ko yake son ya yi, na ce manyan jihohi wadanda suna da girma suna iya kula da kansu, na ce saboda a kara samun zaman lafiya a yi jihohi 12, cikin hanzari muka yi su, hakan ya sa an kara samun zaman lafiya, kuma muna kan son mu kara wadansu jihohin, aka yi mani murabus.
Lokacin da su Murtala suka zo sun tarar muna son mu kara zuwa 19 ko kuma abin da bai kai 24 ba, Lardunan da ke Najeriya a lokacin wajen 22 ne.Sai muka ce muna son namu ya kai 19 ko fiye, amma kuma ba 22 ba, kamar na ‘yan mulkin mallaka, to abin da aka yi ke nan. Ana nan kuma su Babangida suka zo suka yi nasu, shi ma Abacha ya zo ya yi nasa, abin ya zo ya zama 36. Idan muka ce mu yi wadansu jihohi, to zai zama kamar na kabilu ke nan, misali, Hausawa su ce suna son nasu, Nufawa suna son nasu, Tibi suna son nasu, to idan abin ya zama haka,wannan to ba daidai ba ne. Yadda muka yi jihohi na farko ya kamata su zamo kamar yadda Najeriya take ne.Ya zamo kowace jiha akwai kabilu daban-daban domin a samu hadin kai, amma ba wai a yi jihohi na ainihin kabilu ba, wannan zai kawo rarrabuwar kawuna, wannan ba dai dai bane.
Saboda haka gaskiya ni ban goyi bayan hakan ba. Amma idan abin da siyasa tace ne abin da jama’a suke so, kuma dokar kasa ta yarda da hakan, to shikenan sai a yi hakan idan dai zai samar da zaman lafiya. Amma ni dai ina ganin wadanda muke da su yanzu sun isa, domin idan aka kara wadansu to kudin da za a batar suna da yawa, kuma ba za a samu abubuwan da za su taimaka wa jama’a ba.
Aminiya:Yau cin hanci da rashawa ya yi yawa a Najeriya, me kake ganin ya kawo haka?
Gowon:Wannan zancen cin hanci akwai shi da yawa, yau kusan dukkan duniya akwai shi, amma mu a nan Najeriya mun fi fadin abin da ba daidai ba game da wannan batun, ban ce wai babu wannan cin hancin ba, amma cin hanci yana cikin masu bayarwa da masu karba, a gaskiya kowace gwamnati ta zo takan ce tana son ta kashe wannan abin, amma daga baya sai a ga munanan abubuwa suna faruwa, musammam ma daga wadanda suke shugabancin kasa, wannan kam bai kyautu ba,yakamata kowannenmu, babba da karami, talakawa da masu arziki, mu rika yin abubuwa cikin gaskiya da tsoron Allah.Mu hana wannan cutar da muke wa juna, musammam wadanda suke kara wa kansu abin da yakamata jama’a su samu.
Aminiya:Yaya kake ganin za a tinkari tashe-tashen hankulan da suke da alaka da addini irin su Boko Haram?
Gowon:Wadanda suka fara wannan abin (Boko Haram) sun ce wai suna yi ne saboda musulunci, ni wannan abin ya bata mini rai, wane irin musulunci ne suke yi, sun zo suna yayyanka mutane? Musammam ma wadanda ba musulmi ba, irin abubuwan da suka yi ke nan a can wajen su Michika da dai sauransu. Na ga wadansu hotuna inda suke yanka mutane kamar awaki, kai wannan ya bata sunan musuluncin da muka girma da shi muka san yadda yake, kuma manya ba su yi magana da da wuri ba, na ga abin da suka yi wa marigayi Sarkin Kano, na ji abin da shi shugabansu yake cewa game da sabon Sarkin Kano na yanzu Sanusi, kai wannan abu nasu babu kyau ko kadan.
Aminiya: Abin da ake cewa cin hanci da rashawa ne ya shiga cikin sojojin Najeriya har suka kasa yakar su har ana zargin cewa akwai hannun wadansu sojojin Najeriya a ciki, me za ka ce game da wannan?
Gowon:Na ji wannan amma amma ni ban yarda ba, na ji wai babban hafsan soja, wani Ihejirika, wai ya yi cin hanci da rashawa, kai ni dai ban yarda da wannan ba, wannan duk ba shi ba ne. Kuma na ji cewa wai Jonathan yana da hannu kuma Igbo ne suke rama abin da aka yi musu lokacin yakin basasa, wannan ba gaskiya ba ne, ba zan yarda da wannan ba ko kadan, ko wa ya fadi haka ba zan yarda da shi ba.