“Ni ne gwamna na farko a Najeriya da ya yi shekara 8 a mulki bai mallaki gidan kansa ba”
Tsohon gwamnan ya ce duk wanda bai yadda da zancensa ba zai iya bincikawa don tabbatar da abin da ya faɗa.
Sakataren Jam’iyyar ADC na Ƙasa, Rauf Aregbesola, ya ce shi ne gwamna na farko a tarihin Najeriya da ya yi shekaru takwas a kan mulki ba tare da mallaki gidan kansa ba.
A cikin wani bidiyo da aka wallafa a ranar Laraba, tsohon gwamnan Jihar Osun, ya ce ya zauna a gidan wani abokinsa tsawon shekarun da ya yi a kan mulki.
- An yi wa wata mata ɗaurin wata 6 kan aikata damfara a Borno
- Matatar Dangote ta dawo sayar da fetur da Naira
Ya ce, “Ni ne gwamna na farko a Najeriya da ya yi shekara takwas a kan mulki ba tare da mallakar gida ba.
“Na zauna a gidan abokina lokacin da nake mulkar jihata a matsayin gwamna. Duk wanda bai yarda ba, ya fito ya nuna gidan da na mallaka.”
Aregbesola, wanda a baya ya kasance na hannun daman Shugaba Bola Tinubu, ya yi wa’adi biyu a matsayin gwamnan Jihar Osun kafin ya zama Ministan Harkokin Cikin Gida a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari.
Ya ce a lokacin da yake gwamna, gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen rage talauci, rage yunwa da rashin aikin yi.
Ya ƙara da cewa ya inganta harkokin lafiya da ilimi, da kuma tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a faɗin jihar.