Ni ne na farko da wani hakimi ya nada Gwagware a Masarautar Katsina – Murtala Gwagware
Sarautar Gwagware sarauta ce ta Mayaka a masarautar Katsina. Kamar yadda marigayi Dokta Mamman Shata ya ce, “Maganar yaki na tunda can su Gwagware Habu suna Katsina,” a cikin wakarsa ta Allah Raya Jihar Katsina. Bisa ga abin da tarihi ya nuna, an fara samun wannan suna ko mukami na Gwagware daga kan Gwagware Habu […]
Sarautar Gwagware sarauta ce ta Mayaka a masarautar Katsina. Kamar yadda marigayi Dokta Mamman Shata ya ce, “Maganar yaki na tunda can su Gwagware Habu suna Katsina,” a cikin wakarsa ta Allah Raya Jihar Katsina.
Bisa ga abin da tarihi ya nuna, an fara samun wannan suna ko mukami na Gwagware daga kan Gwagware Habu tun a lokacin mulkin Dallazawa. Ko da akwai wani wanda ya taba samun wannan suna a baya kafin shi Habu, to abin bai yi fice ba kamar a zamaninsa, wancan zamani kuma an san ana yake-yake a tsakanin sarakuna da dauloli bisa dalilan ko dai fadada kasa ko kamen bayi. Ita wannan sarauta ta Gwagware kamar yadda tarihi ya nuna, ba a yin ta sai ga barde wanda ya shahara a fagen yaki. Yana yin wasu abubuwa da ba kowane mayaki ke yin su ba a fagen daga. Mayaki ne wanda ya saba kawo wa Sarki tsaraba a duk lokacin da ya fita koda ba a fagen yaki ba ne. Daga cikin irin tsarabar da wannan mayaki kan kawo wa Sarki akwai bayi da dabbobi da sauransu.
Alhaji Murtala Ibrahim mai kimanin shekara 43, ya bayyana yadda ya samu wannan sarauta ta Gwagware a karkashin Hakimi ba karkashin Sarki ba.
“Farko dai ni haifaffen kusa da wani tafki ne da ake kira da sunan Gwagware wanda a wani kauli ake cewa, asalin sunan tafkin ya samo ne daga shi Gwagware Habu wanda ake cewa a wancan lokacin ya zauna a wannan yanki ne daga cikin birni. Amma a yanzu zuriyarsa na zaune a Unguwar ’Yar’aduwa da ke cikin garin Katsina. Ka san mutanen cikin birni sai da harkar kasuwanci, to na taso a cikin wannan harka ta kasuwanci baya ga neman ilimi da aka yi duka biyun, wato na addini da na zamani. To wannan harka ta kasuwanci ta hada ni da Sarkin Gabas, Hakimin Mani Alhaji Babani Isa. Yakan zo sayayya a shagonmu wanda muka sanya wa sunan Gwagware domin muna takama da wannan suna. In ya zo ina girmama shi matuka,” inji shi.
Alhaji Murtala ya ce, ba zai manta da ranar da aka nada Dokta Dikko Radda a matsayin Gwagwaren Katsina ba, wanda marigayi Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Kabir Usman Nagogo ya yi. Ina shago wajen kasuwancina sai kawai na ga kiran Hakimi. Bayan mun gaisa sai yake ce mini, ashe kai wannan suna ko sarautar tana da tarihi da tasiri haka, ka bari ta kubce maka? (A cikin dariya ya ce): “Saboda haka, ni na ba ka wannan sarauta a masarauta ta Mani. Dukan irin abin da na ji a kan sarautar na ga ka cancance ta, duk kuwa da cewa, ba lokacin yakin ba ne a yanzu, amma kana yaki da zuciyarka wajen girmama jama’a da ba kowa hakkinsa, ga kuma kokarin dogaro da kai da kuma taimaka wa jama’a.” Abin na dauka da farko kamar irin ’yan wasannin da ya saba yi da jama’a, domin mutum ne mai son jama’a,” inji Gwagwaren Mani.
Gwagwaren ya ce, an yi masa wannan nadi ne a ranar 16 ga watan Mayun shekarar 2009 a fadar Mai girma Sarkin Gabas da ke garin Mani.
To mene ne aikinsa a ita wannan masarauta ta Hakimi?
“To ina cikin Kansilolin Hakimi, ma’ana ina cikin masu ba shi shawara kuma mai wakiltarsa a wasu ayyuka ko wasu wurare da aka gayyace shi bai da halin zuwa. To yakan tura ni don in wakilce shi.
Kuma ko ni a yanzu ban iya cewa, ga iyakar inda na je da sunan wakilinsa. Kuma tun daga ranar da aka nada ni zuwa yau, kimanin shekara 10 ke nan, ban taba ganin wani abu na bacin rai ba ko ya ce yau na yi wani abin da ba daidai ba. Kuma wannan sarauta ba ta hana ni yin duk wata hidima tawa ba. Kuma a gaskiya muna bakin iyawarmu na ganin cewa, ba mu ba shi kunya ba. Ga Hawan Sallah da ake yi kadai ya isa jama’a su shaida haka. Gaskiya, duk da nauyin da sarautar take da shi, ina jin dadinta domin ko ba komai, sunan mahaifata ke nan, sannan sunan inda nake neman abinci ne, sai kuma ga shi ina rike da sarautar wadda na zamo mai riƙe da ita na farko a karkashin wani hakimi a Masarautar Katsina, wanda shi ma shi ne na farko da ya yi irin wannan nadi bayan ya samo izinin daga Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.