Ni zan jagoranci yi wa Tinubu kamfe a sabuwar shekara —Buhari
Buhari ya yi batan dabo tun bayan kaddamar da yakin neman zaben APC a Jos.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shaida wa dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, cewa da kansa zai jagoranci masa yakin neman zabe da zarar an shiga sabuwar shekara.
Hadimin Buhari kan kafafen zamani, Bashir Ahmad, ya ce, Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin dan takarar a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba.
- Ba mu san yawan sabbin takardun kudin da aka buga ba —CBN
- Tsoffin kansiloli 360 sun yi Al’kunuti kan hakkinsu a hannun Gwamnatin Kano
Sai dai babu wani cikakken bayani game da abin da suka tattauna a ganawar tasu; Kazalika, a ranar Laraba Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya ziyarci Tinubu a gidansa da ke Abuja.
Shugaba Buhari, ya ce yakin neman zaben APXC zai fi kafa tarihi idan aka duba da yadda ’yan jam’iyyun adawa ke kame-kame da sunan yakin neman zabe.
A cewar kakain Buhari, Malam Garba Shehu, APC na da yakinin lashe dukkanin zabukan da ke tafe.
Buhari ya jadadda wa APC da dan takarar nata cikakken goyon bayansa gare su a zaben da ke tafe.
Buhari dai ya yi batan dabo tun bayan da APC ta kaddamar da yakin neman zabenta a Jos, babban birnin Jihar Filato.
Sai dai Shehu ya ce shugaban na sane da aikin da ke gaban jam’iyyar, duba da tarin ayyukan da ke gabansa a matsayin shugaban kasa, wanda suke bukatar ya ba su kulawa.
A yayin ganawar da Buhari ya yi da wasu ’yan Najeriya mazauna birnin Washington DC na Kasar Amurka a ziyarar da ya kai, ya nanata cewa da zarar an shiga sabuwar shekara zai ja ragamar kamfen din APC.