Nice ta soma zawarcin Pochettino
Sai dai akwai matsalar albashi da kocin ke bukata a cinikayyar tasu.
Kungiyar Kwallon Kafa ta Nice da ke Faransa ta fara zawarcin tsohon kocin Kungiyar PSG, Mauricio Pochettino.
Kungiyar tana neman tsohon kocin na Tottenham ne domin canja kocinta na yanzu, Lucien Fabre wanda take ganin kamar ba zai iya aikin ba.
- ECOWAS ta kara wa Guinea takunkumi kan rashin mika wa farar hula mulki
- Dauda Dare ya sake lashe zaben dan takarar gwamnan PDP a Zamfara
Pochettino koci ne kwararre musamman wajen gina kungiya, lura da lokacinsa a Tottenham, inda ya gina kungiyar ta kai ga zuwa wasan karshe na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai a shekarar 2019, kafin Kungiyar Liverpool ta doke ta da ci 2-0.
Sai dai akwai matsalar albashi da kocin ke bukata a cinikayyar tasu.
Sannan akwai batun cewa kocin bai son komawa Gasar Ligue 1 ta Faransa bayan sallamarsa da PSG ta yi, wadda ita ce babbar kungiya a kasar baki daya.
Duk da cewa an yi ta nuna masa yatsa na rashin lashe kofi a lokacinsa a Tottenham, ya lashe kofuna uku a PSG kafin su raba gari.
A Gasar Faransa ta Ligue 1, ya lashe kofi a shekarar 2022, sannan ya lashe Kofin Coupe de France a shekarar 2021, sai Kofin Trophees des Champion a shekarar 2020.
Tun da PSG ta sallame shi yake zauna babu aiki, kuma ba tare da wata babbar kungiya ta taya shi ba.