NIHORT ta horar da manoman tumatur a Arewa Maso Gabas

An zabo manoman daga jihohi shida na shiyyar Arewa Maso Gabas.

NIHORT ta horar da manoman tumatur a Arewa Maso Gabas

Wasu daga cikin manoman a lokacin daukar horon

Cibiyar Nazarin Koyar da Harkokin Noman Tsirrai Ta Kasa, National Horticultural Research Institute (NIHORT) ta horar da manoman tumatir 40 a shiyar Arewa maso Gabas, kan sanin yadda za a sarrafa sinadaran da ke jikinsa.

Da yake jawabi a wajen taron horarwar a Gombe, Shugaban Kwamitin Gudanarwar Cibiyar, Manjo-Janar Mohammad Garba (mai ritaya), cewa ya yi horon na da fa’ida wajen cimma muradun samar da ayyukan yi wajen bunkasa tattalin arzikin kayan lambu musamman tumatir.

A cewarsa, tumatir yana saurin samar da bunkasar tattalin arzikin kasa ta hanyoyin da ake sarrafa shi daban-daban tun daga danyensa har zuwa lokacin da ya bushe.

A nasa tsokacin, Babban Baraktan Cibiyar ta NIHORT, Dokta Abayomi A. Olaniyan, ya ce yanzu haka a Najeriya tumatir din da ake samarwa ya karu zuwa ton miliyan 2.3.

Ya ce a shekaru biyu baya ana samar da ton miliyan 1.8 kadai, kuma bukatarsa da ake da shi a kasa har yanzu yana nan a kan ton miliyan uku.

A jawabansu, manoman tumatur da suka halarci taron horarwar da muka zanta da su, Musa Jibrin da Madam Agaku Eunice, sun bayyana cewa sun samu karin ilimi a horon kuma za su aiwatar da abin da suka koya a gonakinsu don rubanya yabanyarsu.

A cewar Madam Agaku, da tana noma tumatir ne ba tare da sanin sahihancin irin da take shukawa ba, amma yanzu ta sani.

Manoman an zabo su ne daga jihohi shida na Arewa Maso Gabas.