Nijar: ECOWAS ta yi watsi da gwamnatin rikon kwaryar shekara 3

ECOWAS ta yi watsi da bukatar sojojin Nijar na kafa gwamnatin rikon kwarya ta shekara uku kafin dawowar mulkin fara hula

Nijar: ECOWAS ta yi watsi da gwamnatin rikon kwaryar shekara 3

Kungiyar rainon tattalin arzikin yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi watsi da bukatar masu juyin mulkin Jamhuriyar Nijar na kafa gwamnatin rikon kwarya ta shekara uku kafin dawowar mulkin fara hula a kasar.

Shugaban sabuwar gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani dai ya sanar cewa zai jinkirta dawowar gwamnatin farar hula kasar zuwa nan da shekaru uku.

A gefe guda kuma ECOWAS na tunanin amfani da karfin soji, idan ya zama dole, domin kifar da juyin mulkin ta dawo da Shugaba Mohamed Bazoum kan kujerarsa, idan sojojin da suka yi masa juyin mulki sun bijire wa hanyoyin diflomasiyya.

Kwamishinan harkokin tsaro da siyasa na ECOWAS, Abdel-Fatau Musah, ya bayyana shirin sojojin Nijar na kafa gwamnatin kwarya ta shekara uku da cewa wasan yara da kungiyar ba za ta taba amincewa da shi ba.

“So muke a dawo da halastacciyar gwamnati nan ba da jimawa ba, sannan ba wai mun jingine shirin daukar matakin soji ba ne idan ta kama,” in ji shi, a hirarsa da Aljazeera.

– ‘Za ku gane kurenku’ –

A wata hirat talabijin da aka yi da Janar Tchiani ya zargi ECOWAS da hada baki da wasu kasashen waje da bai ambata ba, wajen rundunar mamayar kasarsa.

Amma ya ce, “Duk wanda ya kawo mana hari to zai yaba wa aya zaki, sabanin yadda yake tunani.”

Shugabannin kasashen ECOWAS na ganin yanzu ne ya fi dacewa su dauki mataki, saboda Nijar ce kasa ta hudu ta sojoji suka yi juyin mulkin daga shekarar 2020 zuwa yanzu, bayan Burkina Faso da Guinea da kuma Mali.

Musa ya ce, “Gwamnatin rikon kwarya ta takaitacen lokaci muke so a yi… wadda ba za ta shekara guda ba, sai dai kasa da haka sosai.

“Mun ga irin haka a juyin mulkin da aka yi a shekaru uku da suka gabata. Har yanzu karin lokaci gwamnatocin rikon kwaryan suke neman a ba su, bayan yarjejeniyar da suka kulla da ECOWAS.

“Don haka ba za mu sake shiga wata sabuwar yarjejeniyar da babu ranar da za ta kare ba,” in ji shi.

Rundunar dawo da Bazoum

ECOWAS dai ta amince da kafa rundunar ko-ta-kwana domin dawo da mulkin dimokuradiyya a Nijar, duk da cewa ba ta ayyana ranar da rundunar za ta fara aiki ba.

Har yanzu kungiyar tana bin hanyoyin diflomasiyya inda ta ce matakin soji shi ne zai kasance na karshe idan sojojin sun turje.

Sabanin yadda da farko gwamnatin sojin ta Nijar ta ki ganawa da wakilan ECOWAS, a makon jiya Janar Tchiani ya gana da su, ya kuma ba su damar ganin Bazoum a inda yake tsare tare da iyalansa da fadar shugaban kasa, kan zargin cin amancar kasa.

Bayan ganawar tasu ce aka ga hoton wakilan na ECOWAS tare da Bazoum, wanda shi ne karon farko da aka ga hotonsa tun bayan da sojojin suka kifar da gwamnatinsa a ranar 26 ga watan Yuli.

– Goyon bayan juyin mulki –

A ranar Lahadi dubban al’ummar Nijar sun yi zanga-zangar goyon bayan juyin mulkin a birnin Yamai; duk da cewa sabuwar gwamnatin ta hana zanga-zanga, amma ta amince da na goyon bayan juyin mulkin.

A birin Agadez, daruruwan magoya bayan juyin mulkin sun yi zanga-zangar neman rufe sansanonin sojojin kasashen waje da ke kasar.

Amurka na da sojoji kusan dubu guda a Nijar, Faransa na da 1,500 da suke taimaka wa gwamnatin Bazoum wajen yaki da masu ikirarin jihadi.

Yankin Sahel, inda Nijar take na fama da ’yan tayar da kayar baya masu ikirarin jihadi da ke da alaka da kungiyoyin Al-Qaeda da IS, wadanda sojojin ke cewa gazawar gwamnatocin fararen hula wajen murkushe su ne ya su kwace mulki.

Agajin Burkina Faso

Aminiya ta ruwaito cewa gwamnatin sojin Nijar ta samu agajin tireloli 300 na abinci daga takwararta ta kasar Burkina Faso domin rage mata radadin takunkumin karya tattalin arziki da ECOWAS ta kakaba mata.

Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum a watan da ya gabata ne kasashen Najeriya da Jamhuriyar Benin suka rufe iyakokinsu tare da katse hulda da Nijar domin matsa wa sojojin su mika wa Bazoum kujerarsa su koma bariki.

Amma Burkina Faso wadda ita ma sojoji suka kwace mulki ta gaggauta agaza wa takwararta ta Nijar. Wannan kari ne a kan alkawarin taimako ta fuskar soji da Burkina Faso ita da Mali suka yi wa sojojin Nijar akan duk wata barazana ta bangaren.

Daraktan Kwastam na gwamnatin sojin Nijar, Kanar Adamou Zaroumeye ya tabbatar cewa “manyan motoci kimanin 300  na abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum sun iso” sojoji sun iso birnin Yamai da rakiyar sojoji daga kasar Burkina Faso.

Daya daga cikin direbobin motocin, Seydou Mie Zanaidou, ya ce sun dauko kayan daga yankin Kaya da ke Burkina Faso zuwa Dori da ke gabashin kasar sannan suka tsallaka zuwa Jamhuriyar Nijar ta garin Tera zuwa Yamai.

A makon da ya gabata ne Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi cewa tankunkumin da aka kakaba wa Nijar da kuma rufe iyakokin kasar na kawo cikas ga jigilar abinci da magunguna zuwa kasar.

Wakilin Sakatare Janar na Majalisar a Yammacin Afirka da yankin Sahel, Leonardo Santos Simao, ya roki gwamnatin ta bude kofa domin isar da kayan agaji.

– Yara na cikin tsananin bukata’ –

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar (UNICEF) ya ce rikicin Jamhuriyar Nijar ya kara jefa miliyon yara masu rauni cikin hatsari baya ga wanda a baya kasar ke ciki.

“Sama da yara miliyan biyu ke cikin wannan tsari,” in ji wakilin UNICEF na Nijar Stefano Savi.

Gabanin wannan matsalar, kananan yara miliyan 1.5 ’yan kasa da shekaru biyar ne ake hasashen za su yi fama da matsananciyar yunwa a wannan shekarar.

Kasar Nijar na cikin mafiya talauci a yankin kuma UNICEF na bayyana damuwa kan rashin wutar lantarki a kasar, wanda ke barazana ga adanar alluran rigakafi da ke bukatar kasancewa a kankara.