Nijar, Mali da Burkina Faso sun fice daga ECOWAS
Kasashen sun koka kan yadda ECOWAS ta gaza taimakon su wajen yaki da ta’addanci.
Kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, sun fice daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS).
Kasashen uku, da ke yankin Sahel wadanda sojoji suka hambarar da gwamnatocin dimokuraiyya, sun sanar da yanke hukuncin a ranar Lahadi.
- Ni ne shugabanka idan ka dawo APC – Ganduje ga Kwankwaso
- Hanyoyi 5 na samun saukin tsadar rayuwa a Najeriya
“Bayan shekara 49, al’ummar Burkina Faso, Mali, da Nijar na cikin nadama tare da nuna rashin jin dadi kan yadda kungiyar (ECOWAS) ta bar turbar da aka gina ta a kai,” cewar Kanal Amadou Abdramane, kakakin mulkin sojin Nijar.
Abdramane ya kara da cewa, “Kungiyar ta gaza taimakon wadannan kasashe wajen yaki da ta’addanci da rashin tsaro.”
ECOWAS karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, ta yi barazanar daukar matakin soji idan har gwamnatin Nijar ta ki mika mulki ga farar hula a kasar.
Sai dai gwamnatin sojin Nijar ta ki aminta da sharadin da aka gindaya mata, yayin da kasashen Mali da Burkina Faso suka goya wa Nijar baya.
A ranar Lahadi ne dai, shugabannin kasashen yankin Sahel uku, suka dauki matakin ficewa daga kungiyar ECOWAS.
Tun da farko shugabannin ECOWAS, sun dakatar da kasashen uku bayan juyin mulkin da sojoji suka yi musu.