Nijar: Rugugin harbi ya tayar da ’yan Burkina Faso da tsakar dare
Wata 10 ke nan da sojoji suka suka yi juyin mulki na biyu a Burkina Faso, wadda ita da takwararta Mali da ke hannun sojoji, suke goyon bayan juyin mulkin Nijar
Rugugin harbi da fashewar abubuwa a cikin tsakar dare sun jefa jama’a cikin tashin hankali a Ouagadougou babban binrnin kasar Burkina Faso, makwabaciyar Jamhuriyar Nijar inda sojoji suka yi juyin mulki.
- Mun yanke duk wata alaka ta tsaro da Nijar — Tarayyar Turai
- An cafke Alkalin da ya yi shigar mata yana zana wa budurwarsa jarrabawa
Kimanin wata 10 ke da sojoji suka yi juyin mulki na biyu a Burkina Faso, wadda a halin yanzu ita da takwararta Mali da suke hannun sojoji, suka gargadi kasashen duniya kan daukar matakin soji a kan juyin mulkin Nijar.
Hakan na zuwa ne kwanaki biyar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a makwabciyarta, Jamhuriyar Nijar, wanda ya haifar da takaddama a yankin Sahel da ma duniya.
Wata majiyar tsaro a Burkina Faso ta ce “harbe-harben da aka ji sun takaita ne a wani sansanin sojin sama,” amma ta ce daga bisani kurar ta lafa bayan kimanin awa guda da hakan ya tsayar da harkokin sufuri.
A watan Satumbar 2022 ne Kaftin Ibrahim Traore ya hambarar da Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda ya kifar da gwamnatin zababben Shugaban Kasa, Roch Marc Christian Kabore na Burkin Faso.
Kowanne daga cikin musu juyin mulkin biyu na ikirarin daukar matakin ne saboda gazawar gwamnatin kasar wajen murkushe masu ikirarin jihadi da suk kashe dubban al’ummar kasar, lamarin da ya sa matsalar fadada zuwa Mali a 2015.
Sai dai kuma juye-juyen mulkin sun kawo nakasu ga kokarin kasar na murkushe mayakan masu alaka da kungiyoyin Al-Qaeda da kuma IS.
AFP ya ruwaio cewa mayakan sun kwace kimanin kashi 40 cikin 100 na kasar, inda suka kashe fararen hula da jami’an tsaro kimanin 16,000, wadanda kimamin 5,000 daga cikinsu a bana aka kashe su.
Akalla mutum miliyan biyu ne suke zaman gudun hijira a cikin kasar a sakamakon wannan matsala.