Nijar ta ayyana zaman makokin kwanaki 3 bayan kisan sojojinta 20
Nijar ta sanar da zaman makoki na kwanaki uku, sakamakon kisan sojojin kasar 20 da farar hula guda a yammacin kasar, mai fama da kungiyoyi masu ikirarin jihadi.
Gwamnatn Nijar ta ayyana zaman makokin kwanaki uku sakamakon kisan sojojin kasar 20 da farar hula guda a yammacin kasar, mai fama da kungiyoyi masu ikirarin jihadi.
Cikin Sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta karanta ta gidan talabijin na kasar ta ce Hadin gwiwar kungiyoyin ‘yan ta’adda” sun kai wa jami’an tsaro hari a kusa da kauyen Tassia, inda suka kashe sojoji 20 da jikkata wasu 9.
Sanarwar ta ce an jami’an tsaro sun kashe mahara da dama, kuma an tura sojoji ta sama da ta kasa domin zakulo sauran maharan.
Tassia na yankin Tillaberi da ke iyaka da Mali da Burkina Faso inda ‘yan tawaye masu alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS suka kwashe kusan shekaru goma suna tada kayar baya.