Nijar ta kori wasu kamfanonin China 3 daga ƙasar
A shekarar da gabata ce Nijar ta ƙulla yarjejeniyar cefanar da ɗanyen man fetur ta dala miliyan 400 da ake haƙowa a ƙasar.

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta kori manyan jami’an wasu kamfanonin CNPC da WAPCO da SORAZ na China daga ƙasar.
Haka nan, gwamnatin ta kuma soke lasisin wani babban Otel na China da ke birnin Yamai.
- Faɗuwar farashin kayan abinci a watan azumi ta shammace mu – ‘Yan kasuwa
- ’Yan bindiga na neman N30m domin fansar gwarzon gasar Al-Qur’ani a Katsina
Gwamnatin Nijar ɗin na zargin kamfanonin da ƙin mutunta dokokin aiki a ƙasar da ma na yarjejeniyar aiki da suka sanya wa hannu.
Wasu majiyoyi na kusa da gwamnatin sun tabbatar da cewa tun a ranar Larabar da ta gabata Shugaba Janar Abdourahmane Tchiani ya bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga manyan daraktacin kamfanonin CNPC mai aikin haƙar man fetur a Nijar da na kamfanin WAPCO da ke kula da jigilar ɗanyen man Nijar ta bututu zuwa tashar ruwan Cotonou da kuma na babbar matatar mai ta SORAZ su bar ƙasar baki ɗaya.
Majiyoyi na cewa hukumomin ƙasar ta Nijar na zargin kamfanonin na Chinar da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da ƙin mutunta yarjejniyar horas da ma’aikata ‘yan Nijar.
Haka kuma, hukumomin na zargin ci da gumin ma’aikatan Nijar ta hanyar ba su albashin da bai taka kara ya karya ba a gaban takwarorinsu na Chinar da ma shirya makarkashiyar da ta haddasa matsalar karancin man fetur a baya bayan nan a kasar.
Yanzu haka dai ko baya ga korar waɗannan manyan daraktoci na ƙasar China, gwamnatin mulkin sojan Nijar ta kuma sanar da ƙwace lasisin aiki na babban Hotel na SOLUXE mallakar China da ke birnin Yamai.
A ɓangaren ɗaya kuma Gwamnatin Nijar ɗin ta ba da izinin rufe asusun ajiyar kuɗi na babbar matatar mai ta kasa ta SORAZ.
Kawo yanzu dai kasar ta China ba ce uffan ba, haka kuma mahukuntan kamfanonin da abin ya shafa da aka tuntuɓa ba su magantu a kan lamarin ba.
A shekarar da gabata ce Nijar ta ƙulla yarjejeniyar cefanar da ɗanyen man fetur ta dala miliyan 400 da ake haƙowa a ƙasar.
A yayin da wasu ‘yan Nijar ke yaba wa da matakin wasu na ganinsa a matsayin barazana ga makomar hulɗar ƙasar da China da ma tattalin arzikin Nijar ɗin baki ɗaya.