Tirela 300 dauke da kayan abinci sun shiga Nijar daga Burkina Faso
Manyan motoci 300 dauke da kayan abinci daga gwamnatin sojin Burkina Faso sun isa birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar
Jerin gwanon manyan motoci 300 makare da kayan tallafi ga sabuwar gwamnatanin sojin Nijar daga kasar Burkina Faso sun isa Yamai, babban birnin kasar.
Gwamnatin sojin Burnkina Faso ta tura wa takwararta ta Nijar tallafin kayan abinci da sauransu ne domin rage mata radadin takunkumin karya tattalin arziki da kungiyar ECOWAS ta kakaba mata.
- An yanke wa tsohon fira ministan Thailand daurin shekara 8
- NAJERIYA A YAU: Yadda Wike Ya Kaɗa Hantar ’Yan Abuja
Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum a watan da ya gabata ne kasashen Najeriya da Jamhuriyar Benin suka rufe iyakokinsu tare da katse hulda da Nijar domin matsa wa sojojin su mika wa Bazoum kujerarsa su koma bariki.
Amma Burkina Faso wadda ita ma sojoji suka kwace mulki ta gaggauta agaza wa takwararta ta Nijar. Wannan kari ne a kan alkawarin taimako ta fuskar soji da Burkina Faso ita da Mali suka yi wa sojojin Nijar akan duk wata barazana ta bangaren.
Daraktan Kwastam na gwamnatin sojin Nijar, Kanar Adamou Zaroumeye ya tabbatar cewa “manyan motoci kimanin 300 na abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum sun iso” sojoji sun iso birnin Yamai da rakiyar sojoji daga kasar Burkina Faso.