Nijar ta yanke hulda da Najeriya

Gwamnatin sojin Nijar ta ki tattaunawa da wakilan da kungiyar ECOWAS ta tura domin sulhu

Nijar ta yanke hulda da Najeriya

Masu zanga-zangar bikin zagayowar samun ‘yancin Jamhuriyar Nijar a birnin Yamai (Hoto / AFP).

Gwamnatin sojin Nijar ta katse huldar diflomasiyya da Najeriya, Togo, Amurka da kuma ta fuskar tsaro da tsohuwar uwargijiyar kasarsu Faransa.

Kwana biyu ke nan bayan gwamnatin Nijar ta ce babbar makwabciyarta Najeriya ta katse wutar da take ba ta, lamarin da ya sa biranen Yamai, Maradi, Zinder da sauran sassan kasar cikin matasalar wutar lantarki da ba su saba ba a baya.

Gwamnatin sojin Nijar din ta kuma ki ganawa da wakilan da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS), ta tura domin tattaunawa da ita.

Wani daga cikin wakilan ya shada da kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kasa da awa 24 da isarsu birnin Yamai suka baro kasar Nijar, “ko kwana ba mu yi ba,” ballantana ganawa da Janar Abdourahamane Tiani kamar yadda aka tsara.

A ranar Laraba ne ECOWAS ta tura wakilan nata, karkashin jagorancin tsohon shugaban mulki sojin Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, domin tattaunawa da gwamnatin sojin da ta yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki.

Da farko dai gwamnatin Najeriya ta sanar cewa kwamitin na Abdulsalami Abubakar zai gana da Janar Tiani inda zai  gabatar wa gwamnatin sojin da ta yi juyin mulki a Nijar bukatun ECOWAS.

Kungiyar wadda Shugaan Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu yake jagoranta, ta kakaba wa gwamnatin sojin ta Nijar takunkumin karya tattalin arziki, sannan a ranar Lahadi ta ba wa sojojin wa’adin mako guda su mika wa Bazoum mulkinsa.

Nijar: Janar Tchiani ya yi biris da ECOWAS

Tinubu ya ce duk da cewa ECOWAS za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an sasanta matsalar cikin ruwan sanyi, amma idan ta kama kungiyar ta dauki matakin soji.

A ranar Laraba manyan hafsoshin tsaron kasashen ECOWAS suka yi taro a Abuja kan juyin mulkin na Nijar, inda suka yi ittifaki cewa idan abin ya zama babu makawa, za su dauki matakin soji.

Tuni dai Janar Tchiani ya yi watsi da takunkuman da barazanar ECOWAS da manyan kasasehn duniya, inda ya ce cewa duk kasar da ta nemi yin shisshigi a harkokin cikin gidan Jamhuriyar Nijar za ta yaba wa aya zaki a hannun dakarun kasar.

A gefe guda kuma, makwabtan Nijar biyu, Mali da Burkina Faso da suma suke hannun sojojin da suka yi juyin mulki sun yi gargadi cewa duk wanda ya taba sabuwar gwamnatin Nijar to ya shirya yaki da su.

Hasali ma, kasashen biyu tare da Guinea Bissau wadda ita ma take hannun sojoji sun kaurace wa taron da manyan hafsoshin taron ECOWAS suka yi kan juyin mulkin Nijar a Abuja.

Bazoum na neman dauki

Shi kuma Mohamed Bazoum a ranar Alhamis ya rubuta wata wasikar neman a kasashen duniya su taimaka a dawo da shi kan mulki, inda ya ce muddin juyin mulkin da aka yi masa ya yi nasara, to “hakan zai yi mummunan tasiri a yankinmu dama duniya baki daya.”

Jaridar Washington Post, ta wallafa wasikar da Bazoum ya rubuto daga inda sojojin Nijar din ke tsare da shi, inda yake kira ga “Gwamnatin Amurka da daukacin al’ummar duniya su taimaka wajen dawo da zababbiyar gwamnati da kuma doka da oda,” a Nijar.

Karon farko ke nan da Mista Bazoum ya rubuto dogon sako tun bayan da sojin kasarsa suka kifar da gwamnatinsa a ranar 26 ga watan Yuli.